Abzinawa ƙabila, ce da suke a yankunan Kudancin Afrika, musamman ma a kasashen kamar su Nijar inda yawansu ya kai kimanin 2,116,988, Ƙasar Mali yawan su ya kai 536,557, Burkina Faso yawan su ya kai 370,738, sai ƙasar Aljeriya yawan su ya kai 25,000 sai kuma ƙasar Tunusiya inda yawan su ya kai kimanin 2,000.
Hakanan kuma ana samun wasu ƴan kaɗan a Faransa da koma Najeriya. Abzinawa Bororo (Masu Yawo) ne kuma masu arziki. Akasarin Abzinawa sun kasance Musulmai ne.
Al’ummar Abzinawa na daga cikin ƙabilu da dama kamar Soninke, Mende, Bambara, Songhai, Madinka, Mossi da dai sauransu wadanda suka taimaka wajen yin ciniki tsakanin kasashen sahara wanda ya haɗa dauloli na yammacin Afirka.