Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Bauchi) an haife shi a ranar 5 ga watan Oktoba shekarar alif 1958 a Garin Duguri da ke karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi. Ya halarci makarantar firamare ta Duguri da ke Bauchi daga shekarar alif 1965 zuwa 1971 inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko. Bayan haka ya samu gurbin shiga makarantar sakandiren gwamnati ta Bauchi daga shekarar alif 1972 zuwa 1976 inda ya samu nasarar kammala WASCE.
Daga nan ya wuce Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Arewa-maso-Gabas tsakanin shekarar alif 1977 zuwa 1979 don samun takardar shedar ci gaba. Daga nan ne ya sami gurbin karatu a Jami’ar Maiduguri a shekarar alif 1979 sannan ya kammala a shekarar alif 1982 da digiri na biyu a fannin Turanci.
Bala Mohammed ya halarci Kwalejin Gudanar da Ma’aikata ta Najeriya (ASCON) a shekarar alif 1988 don kwas din gudanar da aiki (General Management Course). A shekarar alif 1997, ya halarci wani horon inganta iya aiki a Legas kuma an ba shi takardar shaidar Cibiyar Saye da Sayarwa.
Ya fara aikin jarida kuma ya kai matsayin Editan Labarai na Jaridar Mirage, Jos tsakanin shekarar alif 1982 zuwa 1983. Ya kuma taba zama wakilin Labarai a Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa watao, NAN. Daga nan ne ya koma jaridar Dimokuradiyya inda ya yi aiki a matsayin Editan Jarida na Jahar Benue daga shekarar alif 1983 zuwa 1984.
A shekarar alif 1984, ya bar aikin sa na jarida, inda ya samu aiki a matsayin jami’in gudanarwa a karkashin ma’aikatar harkokin cikin gida ta tarayya Abuja. A cikin shekarar alif 1994, an ƙara masa girma tare da sake tura shi a matsayin Babban Jami’in Gudanarwa a Sakatariyar Majalisar Ministoci na Fadar Shugaban Kasa.
Ya kasance babban jami’in samar da kayayyaki na ma’aikatar ma’adanai ta tarayya daga shekarar alif 1995 zuwa 1997. Ya kai matsayin mataimakin darakta a ma’aikatar wutar lantarki da karafa ta tarayya a shekarar alif 1997. Ya riƙe mukamin har zuwa shekarar alif 1999 inda aka kara masa mukamin mataimakin darakta/SA ga Hon Minister, Federal Ministry of Transport. Ya samu nasarar sauke aikinsa a wannan mukamin daga shekarar alif 1999 zuwa 2003.
Bayan jajircewarsa Bala Mohammed ya samu mukamin Daraktan gudanarwa na Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya a shekarar alif 2003. Daga bisani a watan Satumba na wannan shekarar, ya zama mataimaki na musamman ga hukumar kula da harkokin sufurin jiragen kasa ta Najeriya ga Ministan Sufurin Jiragen Sama na wannan lokacin. A watan Janairu, ya zama Daraktan gudanarwa da Aiyuka na Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya.
Ayyuka da ya yi a lokacin aikin gwamnatin sa suna haɗar da: Mataimakin Sakatare shekarar alif (1984 – 1986); Mataimakin Sakatare a shekarar alif (1987 – 1989); Babban Jami’in Harkokin Kasuwanci a shekarar alif (1989 – 1992); Babban Jami’in Harkokin Kasuwanci a shekarar alif (1992 – 1994); Mataimakin Babban Jami’in Kasuwanci a shekarar alif (1994 – 1995) da Babban Jami’in Samar da kayayyaki a shekarar alif (1995 – 1997).
Wasu ayyuka na wucin gadi da Alhaji Bala Mohammed ya yi a tsakanin shekarun alif 1984 zuwa 2006 sun hada da :
- Sakatare, Kwamitin Gudanarwa kan Sake Shirya Hukumar Tsaron Farar Hula ta Najeriya (Civil Defense); a shekarar alif (1985);
- Sakataren Kwamitin Bincike kan al’amuran da suka haifar da sayewar ‘yan Najeriya, a shekarar alif (1988);
- Sakataren, Kwamitin tsara ka’idojin doka da na gudanarwa kan al’amuran ‘yan Najeriya; a shekarar alif (1988);
- Sakataren, Kwamitin Sashe na aiwatar da gyare-gyaren Ma’aikatun Najeriya, a shekarar alif (1988)
- Sakataren, Kwamitin Tsaro da Sata na Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Tarayya, Abuja a shekarar alif (1989).
An zabi Bala Mohammed a matsayin Sanat a ranar 21 ga Afrilun shekarar 2007 don wakiltar al’ummar mazabar Bauchi ta Kudu. Ya sami kujerar da ake girmamawa a zauren majalisar wakilai ta kasa Bala Mohammed ya kuma halarci tarukan karawa juna sani da suka hada da:
- shugaban kungiyar hada kadarori na ma’aikatar ma’adanai ta kasa;
- Memba, a kwamitin kan rahoton shekara-shekara, a Ma’aikatar Ma’adanai;
- Memba, a kwamitin kan rubuta kasida (Brochure) ta Ma’aikatar Ma’adinai;
- Memba, a Panel, Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya;
- Memba, a kwamitin shugaban kasa kan cajin jadawalin kuɗin fita da ayyuka a ma’aikatar ruwa;
- Memba, a Tawagar Ministocin da aka zaɓa zuwa kasashen Rasha, Birtaniya, Laberiya, Brazil da Turkiyya.
- Memba, a International Maritime Organization Congress.
Ya zama gwamnan jihar Bauchi a ranar 26 ga watan Maris, shekarar 2019. A zaben da aka gwabza, Bala Mohammed, a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP, ya samu kuri’u 515,113 inda ya doke gwamna mai ci a lokacin, Muhammed Abubakar, wanda ya samu kuri’a. 500,625. Bauchi na da mutane 2,462,803 da suka yi rajista a lokacin. Amma masu kada kuri’a 1,143,019 ne aka amince da su a zaben. Bayan ganin ƙoƙarin Al’ummar Bauchi na zaɓen sa, Bala Mohammed ya himmatu wajen ganin ya biya al’ummar Jihar Bauchi tare da kawo dabaru iri-iri da kwazonsa wajen gudanar da ayyukansa.