Cigaba……
HIKAYAR ABDULLAHI MASUNCI DA ABDULLAHI ƊANRUWA
Ɗanruwa ya ce, “Sunana Abdullahi. Duk sa’adda ka zo nan, idan ba ka tarar da ni ba, ka ɗaga murya ka yi kira da ƙarfi, ‘Ina kake ne Abdullahi, ina kake ya kai Ɗanruwa?’ To duk inda nake a cikin ruwa, zan fito zuwa gare ka da hanzari. Kai kuma yaya sunanka?”
Masunci ya amsa, “Ni ma sunana Abdullahi.”
Ɗanruwa ya yi murmushi ya ce, “Yanzu mun zama abokai, ga ka Abdullahin tudu, ni kuma Abdullahin ruwa. Jira ni nan in kawo maka tsarabarmu ta ruwa.” Sai ya faɗa ruwa ya nutse, tun Masunci na ganin motsinsa har ya daina ganin alamarsa.
Da aka daɗe bai fito ba, sai Masunci ya fara zargin kansa bisa ga wannan sakarci da ya yi, yana cewa, “Anya dai zai sake fitowa? Ya dai kalallame ni da daɗin baki ne kurum, ya yi mini wayo na sake shi, yanzu yana can yana mini dariya. Da a ce na ja shi zuwa gida, da na samu kuɗi ta hanyar nuna wa mutane shi. In riƙa bi kasuwa-kasuwa, da gidajen tajirai, ina wasa da shi ana ba ni kuɗi.
Ya zauna nan yana ta nadamar sakin Ɗanruwa, wata zuciya ta ce masa, “Wawancinka ne ya sa ka saki abin da ka kama da komarka.” Yana cikin waɗannan tunane-tunane, sai ga Ɗanruwa ya dawo, hannayensa cike da zinariya da lu’ulu’u da zabarjadi da jauhari iri-iri, ya miƙa masa ya ce, “Karɓi wannan ya kai abokina. Yi haƙuri da shi, ba ni da kwandon da zan zubo maka a ciki.”
Masunci ya karɓa, baki wangame don tsananin murna da mamaki, ya ɗura cikin aljifansa. Ɗanruwa ya ce masa, “Kullum ka zo nan da sassafe, za ka same ni. Kada ka manta kuma idan za ka zo, ka zo mini da kwandon kayan marmari.” Ya yi masa bankwana, ya wuntsila cikin ruwa abinsa.
Masunci ya tattara komarsa ya nufi gari cike da murna, bai zame ko’ina ba sai rumfar mai gurasa, ya ce masa, “Ɗan uwana, yau dai alherin Allah ya sauka gare ni. Lissafa abin da ke kaina na bashi.”
Mai gurasa ya dube shi da kyau, bai ga alamar kifi a cikin burgamin da yake rataye da shi ba, sai ya yi dariya ya ce, “Kai dai ka cika ba’a. Karɓi gurasarka da kuɗin cefane, ka tafi sai ran da Allah ya hore, ka zo mu yi lissafi.”
Ya kawo gurasa da kuɗi zai ba shi, Masunci ya ƙi karɓa ya ce, “Wallahi ɗan uwana, yau dai Allah ya hore mini da abin da zan biya ka kuɗinka.” Ya tura hannu aljihu ya damƙo duwatsun nan masu daraja ya ba mai gurasa, ya ce masa, “Karɓi wannan duka naka ne. Idan kuma kana da kuɗi ranta mini in samu na kashi, kafin na sayar da sauran duwatsun da na samu.”
Mai gurasa ya cika da mamaki, ya kuma yi farin ciki gayar farin ciki da duwatsun da Masunci ya ba shi. Ya tattara duk ɗan cinikin da ya yi na ranar ya ba Masunci, ya kuma cika kwando da gurasa ya aza bisa kansa, ya rufe rumfa ya ce wa Masunci, “Mu tafi in kai maka wannan gida, yanzu kai ne shugabana.”
Suka bi ta kasuwa, Masunci ya sayi nama da kayan marmari da alawa da kayan shaye-shaye da tanɗe-tanɗe da na ƙwalam da maƙulashe, suka nufi gida. Matar Masunci ta karɓi kaya, ta shirya musu abinci da abin sha masu rai da lafiya, suka zauna suka yi ta sharɓar gara suna fyace hanci. Mai gurasa ya manta da rumfarsa da ya rufe. Duk sa’adda Masunci ya ce masa, “Ya ɗan uwana, ka koma ga rumfarka, mutane na can na jira.”
Shi kuma sai ya ce, “Ai abin da ka ba ni yau, ba zan same shi ba, ko da na yi wata guda ina ciniki a rumfata. Don haka gaba ɗaya yinin yau, kai zan yi wa hidima saboda nuna godiyata gare ka.”
Abdullahi Masunci ya ce, “Ai ni ne ya kamata na gode maka saboda taimakona da ka yi lokacin da nake cikin ƙunci.” Suka share yinin ran nan har dare, babu abin da suke yi sai dai su wanke goma su tsoma biyar. Da dare ya soma yi sosai, suka yi sallama da juna, bayan sun ƙulla abota a tsakaninsu. Masunci kuma ya kwashe abin da ya faru duka tsakaninsa da Ɗanruwa ya faɗa wa matarsa.
Matar ta ce, “Allah shi ne mai baiwa. Ina horon ka da ka ɓoye sirrinka daga mutane, kada wannan labari ya kai ga kunnuwan sarakuna, su yi maka zalunci.”
Masunci ya ce, “Ko na ɓoye wa kowa wannan sirri, to ba zan ɓoye miki ba, ba kuma zan ɓoye wa abokina mai gurasa ba.”
Da gari ya waye, tun da jijjifi, Masunci ya ɗauki kwandon da ya cika da kayan marmari tun jiya da yamma, ya nufi bakin teku. Da isarsa sai ya ƙwala kira, “Ina kake ne Abdullahi, ina kake ya kai Ɗanruwa?”
Sai ya ji daga cikin ruwa an ce, “Ga ni nan.” Ɗanruwa ya fito ya karɓi kwando, ya koma cikin ruwa, tsawon sa’a guda bai dawo ba. Can sai ga shi ya komo da kwando cike da duwatsu masu daraja iri-iri. Masunci ya aza kwando bisa kansa ya nufi gari.
Da ya zo rumfar mai gurasa, sai mai gurasa ya ce masa, “Tun ɗazu na toya gurasa arba’in na aika maka gida. Yanzu ma ga wata nan ta musamman kan wuta, idan ta gasu zan cire na kai maka gida da kaina. In tafi kasuwa in sayo maka nama da kayan marmari.”
Masunci ya damƙo ma’adinai daga cikin kwando, har sau uku da hannunsa, ya ba mai gurasa, sa’annan ya wuce gida ya ajiye kwando. Ya ɗauki dutse ɗaya-ɗaya daga nau’in kowane ma’adini ya nufi kasuwar ‘yan jauhari. Ya je ga rumfar wani tajiri, shugaban ‘yan jauhari, ya ce masa, “Kana sayen jauhari?”
Tajiri ya ce, “Ina jauharin?”
Masunci ya miƙa masa dutse ɗaya na zinari da dutse ɗaya na lu’ulu’u da dutse ɗaya na yaƙutu da sauran duwatsun da ya zo da su. Tajiri ya karɓa ya duba, ya kuma dubi Masunci tun daga sama har ƙasa, ya tambaye shi, “Kana da wasu ma’adinan bayan waɗannan?”
Masunci ya ce, “Ina da su kwando guda a gida.”
Tajiri ya ce, “Ina ne gidanka?”
Masunci ya amsa, “A unguwa kaza.”
Da tajiri ya ji unguwar da Masunci ya ambata, unguwar talakawa ce, sai ya yi wa yaransa tsawa, “Ku kama shi! Shi ne ɓarawon da ya sace abin wuyan Sarauniya.”
Nan take mutane suka yi cacukwi da rigar Masunci.
Tajiri ya ce, “Me kuke jira? Ku dake shi!”
Suka far masa da bugu, sai da ya faɗi ƙasa, sannan suka ƙyale shi. Daga nan suka kwashe shi, tajiri ya shige gaba, suka iza ƙeyarsa zuwa fada suna zungurar shi. Wani daga cikin mutanen nan ya ce, “Babu wanda ya sace zinariyar tajiri wane, sai wannan ɓarawo.” Wani ma ya ce, “Ba shakka shi ya sace lu’ulu’un tajiri wane.” Suka dai yi ta ƙaƙalo sace-sacen da aka yi na kayan ma’adinai a garin suna cewa Abudullahi ne ɓarawon. Ya dai yi shiru bai ce musu komai ba, har suka isa fada.
Tajiri ya faɗi gaban Sarki ya yi gaisuwa, sa’annan ya ce, ” Allah ya ba ka nasara, cigiyar da ka ba mu ta sarƙar Sarauniya da aka sace, yau Allah ya ba ni sa’a na kama ɓarawon, ga shi nan. Har ya cire duwatsun abin wuyan ya kawo mini wai in saya.”
Sarki ya ce, “To, madalla.” Ya umurci wani bawa, shugaban babanni, da ya karɓi duwatsun ya shiga da su wajen Uwargida ya tambaye ta ko na abin wuyanta ne.
Za mu ci gaba, in sha Allah.
Marubuci:
Bukar Mada