Ciyar da jariri alkawari ne na kowanne lokaci. Hakanan dama ce don fara kulla alaƙa me karfi tsakanin uwa da danta. Yi la’akari da waɗannan shawarwari don ciyar da jariri.
- SHAYAR DA ZALLAR NONO KO HADI DA MADARA.
Nono shi ne abincin da ya dace ga jariri sabon haihuwa. Idan shayar da zallar nono ta gagara musamman ga mata yara haihuwar farko ana tallafawa da madarar yara dan gudun lalacewar jikin baby, Jarirai masu lafiya basa buƙatar hatsi, ruwa, ruwan ‘ya’yan itace ko wasu ruwaye kuskure ne ba wayewa ko wadata ba ana bawa yaro juice lemukan kwalba.
- ADADIN CIKAKKIYAR SHAYARWA A RANA
Yawancin Jarirai suna bukatar a shayar da su sau 8 zuwa 12 a rana, kuma yana da kyau a samu tazarar awa 2 zuwa 3 tsakanin kowanne shayarwa, alamun baby na bukatar nono sun hada da matsar da hannaye kusa da baki, tsotsar hannu, bugun lebe, haushi da kuka. Da zarar anga wannan alamun ayi kokarin dakatar da komai a shayar da baby.
Lokacin da jariri ya dena shan nono ya saki da kanshi hakan na nufin kodai ya koshi ko yana bukatar hutu ne, a wannan lokacin yana da kyau a bashi minti 1 kafin canza shi zuwa wani nonon. Yayin da jariri ya fara wayo idan an maida shi kan wani nonon nan take zai nuna alamun ya koshi.
- TABBATAR DA BAWA YARO MAGUNGUNAN VITAMIN D
Nono baya fitar da isasshen sinadarin vitamin D dan haka sai ayi shawara da likita ko me maganin gargajiyar da yake da Ilimin sanin abinci ko magungunan da uwa za tayi amfani da su dan karuwar sinadarin vitamin D.
- KULAWA DA CANJE-CANJEN SHAN NONO
Lallai ne uwa tana kula da tsari da yanayin cin abincin yaro musamman na miji dan yafi mace shan nono, lallai ne a kula da karuwar satika suna karuwa yanayin shan nono na karuwa sai a kiyaye.
- TABBATAR DA ANA SHAYARWA A KAN LOKACI
Lallai ne ga mata ma’aikata masu kai yara gidan reno ko masu wadatar da suke daukar masu shayar da yaro su tabbatar ana bin kaidar shayarwa da tsaftace kan nono duk lokacin shayarwa dan gujewa kwayoyin cuta.
BAYAN WATA 6 DA HAIHUWA
Bayan wata 6 da haihuwa, ana bukatar a hadawa yaro wannan hadin da za mu kawo duk bayan awa 6 sauran gab da yake tsakani kuma a bashi nono ya sha:-
- Farar dawa gwangwani 3.
- Jar dawa gwangwani 3.
- Waken suya gwangwani 1.
- Gyada me bargo gwangwani 1.
Ana hade su a nika kar a surfa amma sai an soya gyadar da waken soya sai a tankade dan yayi laushi sosai, sai ana diban table spoon 2 na garin a dama a sheka ruwan zafi 250cl cup a ya zama kunu asa sugar karamin cokali 1 a bawa baby yasha. Lallai koda yaushe sabo za ayi ba a ajiye ruwan zafi a flacks dan ayi da zafin sa sosai ake shekawa dan ya dahu kar ya batawa yaro ciki ya fara kashi.
Bayan shekara daya cif a fara bashi abinci kadan kadan masu gina jiki da narkewa da wuri a ciki ba masu tauri sosai ba.
SHIFA TRADITIONAL MEDICINE