Abduljabbar Nasuru Kabara (an haife shi ranar 7 ga watan Fabrairu shekarar alif 1970) Abduljabbar malamin addinin Islama ne kuma yana ɗaya daga babban malamin Qadiriyya wanda yake zaune a Jihar Kano, Nigeriya.
Mahaifin sa Nasuru Kabara shi ne tsohon shugaban Darikar Qadiriyya ta yammacin Afrika, kuma ƙani ga Karibullah Nasir Kabara magajin mahaifinsu Nasuru Kabara.
An haifi Abduljabbar a garin Kabara da ke cikin birnin Kano a Najeriya, mahaifin sa shine fitaccen shugaban Qadiriyya na Afirka ta Yamma Sheikh Nasir Kabara, sunan mahaifiyarsa Hajiya Hafsah Adussamad, Kuma shine ƙani ga shugaban Qadiriyya ta yammacin Afrika a halin yanzu. Wanda aka fi sani da Qaribullahi Nasuru Kabara, dan uwansa ne ke jagorantar Harkar Qadiriyya a Najeriya tun bayan rasuwar mahaifinsu Sheikh Nasir Kabara a shekara ta alif 1996.
Ya yi makarantar Ma’ahad kamar yadda kowa yake yi daga gidan Kabara, Ya kara karatunsa a Aliya da ATC Gwale, daga baya ya koma Iraƙi don ci gaba da karatunsa, amma a cewar Abduljabbar ya ce ya samu mafi yawan karatunsa a wurinsa mahaifinsa a kusan shekaru 25 na rayuwarsa.
Abduljabbar na ɗaya daga cikin shahararrun malamai mabiyin Qadiriyya inda ya bi sahun mahaifinsa.
Daga baya a wajen shekara ta 2020 zuwa 2021, Ya bayyana kansa a matsayin ɗan Shi’a a wata hira da BBC Hausa. , yana mai cewa “Bayan dogon bincike da na yi ni kadai, sai na gane cewa Shi’a na da karin hujjoji na Nassi a kan Musulunci Sunna ta wannan bangaren”
Ya ce “Ba zan damu kaina ba idan ka kira ni ɗan Shi’a, amma zan damu idan ka kiran ni ɗan Sunna”.
Yanzu haka dai wasu daga ciki jama’ar Kano da kuma gwamnatin Kano sun zarge shi da yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW), wanda hakan ya sanya har zuwa yanzu yana ɗaure a kurkuku.