Muhammadu Bello Kagara 1890 – 1971, malami ne, marubuci kuma ɗan sarauta. Shine marubucin sanannen littafin nan mai suna Gandoki, littafi ne da aka rubuta yayin gasar Adabi wada Rupert East ya shirya. Littafinsa mai suna Ganɗoki an ɗauke shi a matsayin littafi na ɗaya ko na biyu da za a buga a duk faɗin Arewacin Nijeriya, na farko ko na biyu shi ne littafin Ruwan Bagaja na Abubakar Imam.
An haifi Kagara ga iyalan Alkalin Kagara, wanda ake kira Shehu Usmanu. Lokacin da yake karami, iyayensa sun gudu daga Kontagora tare da Sarkin Sudan Nagwamatse don gujewa mamayar sojojin Ingila, domin su kasance karkashinsu.
Kagara ya taba zama dalibi a makarantar Nassarawa, daga baya ya kammala karatunsa, ya koyar da ilimin addinin Islama da na Larabci a kwalejin Katsina har zuwa shekarar alif 1945, kafin ya shiga kwalejin, ya koyar a Makarantar Lardin Zariya.
Daga baya kuma a cikin aikinsa aka ba shi sarautar mahaifinsa, wanda ake kira wali ko Daneji na Katsina sannan ya zama babban alkali na gargajiya a karamar hukumar Katsina.
Munai masa Addu’ar Allah ya kyauta makwanci.