Wannan babi na tarihim Dakta Ganduje mun fara shi ne tun daga Haihuwar sa har zuwa fara aikinsa.
Mai karatu ayi karatu Lafiya.
An haifi Dakta Abdullahi Umar Ganduje ranar 25 ga watan Disamba a shekarar alib 1949 a gidan Alh. umar Sha’aibu shugaban kauyen Ganduje dake karamar hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano
Dakta Ganduje ya fara karatun sa na farko a makarantar Alqur’ani da Islamiyya a kauyensa na Ganduje inda ya samu horo a ilimin Addinin Islama.
Daga baya ya koma hedikwatar karamar hukumarsa inda ya halarci Makarantar Firamare ta Dawakin Tofa daga shekara ta 1956 zuwa 1963.
Dakta Abdullahi Ganduje ya halarci makarantar sakandare ta Gwamnati a Birnin Kudu, a shekara ta 1964 – 1968 Dakta Ganduje yana da matukar son ilimi wanda hakan ya sanya shi halarta makarantu har na zuwa gaba da sakandire.
Yasamu takadar shaidar sa ta NCE Advance Teachers College a tsakanin shekara ta alib 1969 zuwa 1972 bayan haka ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello Zariya don karatun digiri a fannin Ilimin Kimiyya daga 1972 zuwa 1975.
Ganduje yasamu takardar digirinsa na biyu a Jami’ar Bayero dake Kano a shekara alib 1979 bayan nan kuma ya dawo Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar 1984 zuwa 1985 inda ya kuma samun wani digirin na biyu a bangaren gudanarawa.
Ganduje ya kuma hucewa zuwa karatun gaba da digiri na biyu wato (PhD) a Jami’ar Ibadan a shekarar ta 1989 zuwa 1993.
FARA AIKINSA
Dokta. Ganduje ya fara aikinsa na koyarwa a shekara ta alib 1975 a Kwalejin Ole da ke yankin kudu maso-kudu a Najeriya yayin aikinsa na shekara daya na bautawa kasa.
Bayan gama hidimar kasarsa, Dokta. Ganduja ya fara aiki a ma’aikatar ilimi ta jihar kano a matsayin Jami’in Ilimi na II a shekara ta 1976, Amma kuma daga baya a wannan shekarar ya koma (Advance Teachers College Kano) A matsayin lakcara na I a bangaren Ilimin halayya.
Bayan shekaru biyu Dokta. Ganduje yasamu Lakcara I a Jami’ar Bayero dake Kano a shekara ta 1978.
Bayan shekaru biyar da fara aikin Dokta. Ganduje ya fara aiki da (Nornit Limited Kano) a matsayin Manajan Darkta daga 1979 zuwa 1981. a shekarar 1981 ya shiga (Federal Capital Development Authority) a matsayin babban Jami’i mai gudanarwa kuma Daraktan tsare-tsare, Bincike da kuma Kididdig, har zuwa 1993.
A cikin shekaru 17 na aikinsa a FCDA Dokta. Ganduje ya rike mukamai daban-daban a ciki wadanda suka hada da: Development Secretary of Kwalli Development area; Sole Administrator, Abaji Area Council; and Chairman, Gwagwalada area Council. An nada shi Babban Sakataren Zartarwa na FCT da kuma biyan diyya. An nada shi Hon. Kwamishinan ayyuka, gidaje da sufuri na jihar Kano daga Janairun shekara ta 1994 zuwa Nuwamba, 1998.
Ku kasance damu a TARIHIN DAKTA ABDULLAHI UMAR GANDUJE NA BIYU (2)
Masha Allah Don Allah idan Anga Kuskure a Sanar Damu Saimu Gyra.
Mungodiya Da Irin Gyare Gyaren Da Kukeyi Mana Ta Kowace Hanya.