Amfanin ‘Ya’yan Hulba Ga Masu Cutar Diabetics (Ciwon Sugar)

0 185

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Hulba ta kasance daya daga cikin dadaddun magungunan da suka shahara a duniya sama da daruruwan shekaru, Yanzu bincike ya kara tabbatar da cewa yin amfani da ‘YA’YAN HULBA yana ragewa mutum Glucose din da yake cikin jininsa, za ta daidai ta shi In Sha Alláh.

Ya danganta da yanayin matsayin cutar Diabetics din Type 1 ce ko kuma Type 2 ce, sannan kuma yana taimakawa gwajin HbA1c ( Gwajin jinin da ake yiwa masu cutar Diabetics musamman Type 2) ya fito lafiya kalau ya daidai ta jinin yadda yakamata da YARDAR ALLAH.

Kuma matukar kana Amfani da wannan hadin, sai kaje asibiti a duba ka, an tabbata za a samu sauyi kuma kasamu lafiya ingantacciya da Yardar ALLAH.

YA ZA AYI ANFANI DA SHI ?

Za a samo ‘ya’yan Hulba dinne cokali daya ( irin cokalin cin abinci dai), sai a zuba a cikin wani kofi madaidaici ( Kamar Moda), sai a zuba ruwa acikin kofin, sai a samo iccen CINNAMON (Girfa/Qirfa) iya tsawon yatsan hannunka sai a sanya shi a cikin kofin da yake dauke da ruwa da Ya’yan Hulba din, sai a rufe kofin.

Sai a barshi ya kwana a jike, da safe kafin mutum yaci komai sai ya shanye shi gaba daya, kullum mutum zai rika yin haka ne har tsawon Wata 3.

Kuma mutum ya tabbatar ya kiyaye abincin da likitansa yabashi shawarar ci ko kauracewa.

Mutum yatabbatar ya rage shan zaqi da kayan zaqi har tsawon watannin nannan 3 lokacin da yake amfani da wannan hadin.

GARGADI :

  • Mace mai ciki da mai shayarwa kar suyi amfani da wannan hadin.
  • Duk mutumin da yake da wata matsalar jini ko aka dorashi akan shan wani magani da ya danganci jini, shi ma ya kauracewa amfani da wannan hadin har sai ya tambayi likitansa. WALLAHU A’ALAM.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »