WA YE BAWA JAN GWARZO???
Bawa Jan Gwarzo wanda sunansa na gaskiya Umaru Dogo, shi kaɗai mahaifiyarsa ta haifa, yana da ƴan uwa guda goma sha ɗaya, kuma Allah shi ya zaɓa a cikinsu ya bawa sarauta.
Sunan mahaifinsa Amadu, wanda ake kiran sa da Almada, bayan rasuwarsa ne jama’a daga cikin ma su mulki su ka nuna cewa sun fi ƙaunar a ba wa Bawa Jan Gwarzo sarauta.
Dalilin wannan suna na Bawa Jan Gwarzo kuwa shi ne, ya kasance mutum ne shi mai yawan Bautawa Allah da roƙon Allah akan ya bashi sarautar da zai zamana ya fi ƙarfin duk wani Namiji mutum da dabba da ke nahiyarsa.
Shekara goma ya ɗauka ya na Bautawa Allah, duk ranar juma’a yakan fito ya je masallaci ai sallar Juma’a dashi ya koma ba tare da ya yi hira da kowa ba, bayan ya fito ne daga inda ya ke bautar Allah (bayan shekara 10) sai Ƙaninsa ya ce lallai Bawa ka zama Jan Gwarzo.
Ana naɗa shi sarauta sai ya kira duk sarakunan ƙasar Hausa da su Nupe da yankin Keffi da Nijar, ya ce da su ” A zo bikin sarautar sa, a wurin naɗin ya ce da su “To daga yau kada a kuma yaƙi a tsakanin daula da daula, Hausa ta koma ɗaya ƴan uwan juna ne, don haka ba maganar yaƙi a tsakanin ƴan uwa”.
Bawa Jan Gwarzo yana ɗaya daga cikin waɗan da su ka bawa Ɗan fodiyo agaji na wurin zama harma ya kai Ɗansa Yumfa wajen Ɗan Fodiyo don ya yi karatu.
A tarihin Bawa Jan Gwarzo bai taɓa yaƙi da ko wacce daula ba har ya koma ga Allah, saboda shi mutum ne mai tsoron Allah da rashin son zubda jini, kuma Allah ya amsa masa roƙonsa, sai da ya rasu sannan abubuwa su ka lalace.
Tarihi ya zo akan ƴarsa ta gane ya rasu ne da ta ji Zakara ya yi Cara, anan ta ce “Tabbas Baba Ya kwanta dama”.
Sau uku ya fita rangadi a rayuwar mulkinsa:
1- Ya yi wajen Nijar a rangadi.
2- Bayan wasu shekaru ya ziyarci Ƙasashen Hausa.
3- Sai kuma na ƙarshe inda ya yi rangadi wajajen yankin Kwara.
Ya yi shekara 82 a duniya, inda ya yi mulki na tsawan shekara ashirin da biyu.
Kafin Ɗan fodiyo ya ci Gobir da yaƙi lokacin Muh’d Yunfa sai da ya yi shekara bakwai ana gwabza yaƙi sannan aka samu nasara akan sa, bayan da akai masa taran dangi da sojojin ƙasashen da aka ci su da yaƙi na ƙasar Hausa.
Wannan shi ne tarihin Bawa Jan Gwarzo a taƙaice.
Marubuci: Gabari Abba