An haifi Dauda Lawal a ranar 2 ga watan Satumbar shekarar alif 1965, a garin Gusau, shi ne ɗa na 3 a wajen mahaifinsa Lawal Muhammad Dare. Tun yana karami aka kai shi gidan kakanninsa na wajen uwa da ke kauyen Guga a jihar Katsina inda ya yi karatun firamare, sannan ya tafi Sakandaren Gwamnati da ke Kankia domin yin karatunsa na Sakandare.
Lawal ya kammala karatun digirinsa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello a shekarar alif 1987 da digiri na farko a fannin Kimiyyar siyasa, ya kuma samin digirin sa na 2 (M.Sc). a fannin kimiyyar siyasa da huldar ƙasa da ƙasa daga jami’ar Ahmadu Bello a shekarar alif 1992, kuma ya yi digirin digirgir wato (PhD) a fannin kasuwanci daga Jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato.
Lawal ya ci gaba da ƙarin neman ilimi ta hanyar daukar kwasa-kwasai a manyan jami’o’i da suka hada da Makarantar Koyon Tattalin Arziki ta Landan, Makarantar Kasuwanci ta Harvard. , Makarantar Kasuwanci a Jami’ar Oxford, Massachusetts, da ke Amurka; Makarantar Kasuwanci ta Wharton, da ke Pennsylvania; Kwalejin Ƙasa ta Duniya, da ke London; da kuma Makarantar Kasuwanci dake Legas da sauransu.
Dauda Lawal Dare ya yi aiki a matsayin jami’in ilimin siyasa a Hukumar Tattalin arziki ta Najeriya. A shekarar alif 1989, ya zama mataimakin babban manaja lokacin da ya shiga Westex Nigeria Limited.
A cikin shekarar alif 1994, an nada shi a matsayin mataimaki na ofishin jakadanci (immigration), daga baya kuma babban jami’in hulda da jama’a, a ofishin Jakadancin Najeriya, da ke Washington, D.C., Amurka.
A shekarar ta 2003 ya koma bankin First Bank Nigeria Plc a matsayin manajan hulda. A shekarar 2011, an kara masa girma zuwa mukamin mataimakin shugaban bankin bangaren Arewa, wato North of First Bank of Nigeria Plc, bayan ya yi ayyuka da dama. A shekarar 2012, ya zama babban darakta, na North of First Bank of Nigeria Plc.
Daga baya Dauda Lawal ya shiga siyasa inda ya tsaya takarar gwamnan jihar zamfara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a shekarar 2018 amma ya sha kaye a hannun Idris Shehu Mukhtar.
A zaben gwamnan jihar Zamfara na shekarar 2023, ya tsaya takarar gwamnan jihar zamfara a karkashin jam’iyyar PDP, kuma ya samu nasarar cin zaben.