HIKAYAR ABDULLAHI MASUNCI DA ABDULLAHI ƊANRUWA
Masunci bai gushe ba, tsawon kwanaki arba’in, yana zuwa bakin teku kullum, tun hudowar rana har faɗuwarta, amma Allah bai nufe shi da kama kifi ko ɗaya ba. Kuma kullum sai mai gurasa ya ba shi gurasa da nusufi goma na cefane ba tare da ya taɓa canja masa fuska ko ya tambaye shi kifi ba. Bai kuma taɓa ƙyale shi yana jira kamar yadda yakan yi wa sauran mutane ba.
Duk lokacin da Masunci ya ce masa, “Lissafa abin da kake bi na, mu gani.” Sai mai gurasa ya ce, “Bari sai sadda Allah ya hore maka mu lissafa duka.” Idan Masunci ya ji haka sai ya yi ta gode masa, bisa ga wannan karimci. Ya kasance yana sanya masa albarka duk lokacin da zai wuce gida.
A kwana na arba’in da ɗaya Abdullahi ya ce wa matarsa, “Ni kam na yi nufin tsinka wannan koma, ko na huta wa kaina da wahalar duniya!”
Matar ta tambaye shi cikin mamaki, “Don me za ka aikata wannan ɗanyen aiki?”
Masunci ya ce, “Saboda ga dukkan alamu rabona ya ƙare a cikin wannan sana’a ta kamun kifi. Har yaushe zan daina jin kunyar mai gurasa bisa ga bashin da yake ɗibga mini kullum. Ni kam ba zan ƙara zuwa teku ba, ballantana har na bi ta gaban rumfarsa ya gan ni, tun da babu wata hanya sai ta nan. Duk sadda ya ƙyalla idonsa ya gan ni, sai ya kira ni ya ba ni gurasa da nusufi goma. Ba zai yiwu na ci gaba da karɓar bashinsa ba.”
Matar ta ce, “Ai sai ka gode wa Allah da ya sanya soyayyarka cikin zuciyar mai gurasa, ga shi muna samun abinci ta hannunsa kullum. Allah da ya toshe maka hanyar samu daga teku, sai ya buɗe maka wata hanyar abinci ta hannun mai gurasa, to mene ne aibu ga wannan?”
Masunci ya ce, “Na tara kuɗinsa da yawa a kaina, ta yaya zan biya shi idan ya nemi abinsa?”
Matar ta ce, “Ya taɓa tambayarka ne, ko ya taɓa yi maka wata baƙar magana?”
Masunci ya amsa, “Wallahi ko ɗaya, duk ma sadda na ce ya lissafa abin da yake bi na, sai ya ƙi, ya ce sai sadda Allah ya hore mani.”
Matar ta ce, “To, ka gani, kada ka dami kanka. Idan har ya gaji ya tambaye ka kuɗinsa, ka ce masa, ɗan jinkirta mini dai har Allah ya hore, kamar yadda muke ta addu’a ni da kai.'”
Masunci ya dubi matarsa ya ce, “To yaushe Allah zai horen?”
Matar ta ce masa, “Baiwar Allah ai yawa gare ta. Yakan ba da ita ga bawa, ta inda bawan bai yi tsammani ba. Kai dai mayar da lamarinka ga Allah.”
Masunci ya ce, “Lallai kin faɗi gaskiya.”
Ya ɗauki komarsa cikin ƙwarin gwiwar abin da matarsa ta faɗa, ya mayar da lamurransa ga Ubangijin talikai. Ya nufi teku yana addu’a cikin ransa, ya nemi gafararsa bisa ga kuskuren da ya yi a baya, sa’annan ya yi addu’a, “Allah ka nufe ni da kama ko da kifi ɗaya ne da zan rage bashin mai gurasa da ke kaina.”
Da ya isa bakin teku sai ya jefa komarsa cikin ruwa. Lokacin da zai jawo ta, sai ya ji ta faye nauyi. Ya taƙarƙare da dukkan ƙarfinsa, ya jawo ta da kyar yana nishi. Da ya fito da ita waje ya duba, sai ya ga mushen jaki a ciki, wanda ya kumbura yana shirin fashewa. Nan take wurin ya gume da ɗoyi.
Masunci ya fitar da mataccen jakin, ya wanke komarsa yana cewa, “Babu tsimi babu dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki. Na faɗa wa matata rabona ya ƙare a cikin ruwa, zan bar wannan sana’a, amma ta ce na haƙura na ci gaba, Allah zai koro mini da arzikina. Yanzu wannan mataccen jakin ne arzikina!?” Ransa idan ya yi dubu, ya ɓaci.
Ya naɗe komarsa ya bar wannan wuri, saboda warin mushen jakin da ke damunsa, ya nufi wani wuri daban ya sake jefa koma tasa, ya jira tsawon sa’a guda, sa’annan ya fara kicikicin jawo ta waje. Ya ji ta da nauyi fiye da fari. Ya ce a cikin ransa, “A’aha, yau kuma matattun jakai zan yi ta tsamowa a cikin ruwa.”
Ya dai taƙarƙare da jan raga. Yana ja yana nishi, yana cije baki don nauyi. Ya ji kamar jijiyoyin hannunsa za su tsinke, jini ya kwanta a tafukan hannunsa. Da kyar da jiɓin goshi ya fito da ragar nan waje. Ko da ya duba sai ya ga wani gwabjejen ƙaton mutum a ciki, duk ragar ta nannaɗe shi. Sai ya yi tsammani irin aljanun nan ne da aka ce Annabi Sulaimanu na ɗaurewa a cikin battar baƙin ƙarfe, yana jefa su cikin teku.
Yanzu kuma saboda tsawon zamani, battocin sun soma lalacewa, aljanun na fitowa. Sai ya zaci ɗaya daga cikin aljanun ne ya faɗa komarsa. Don haka sai ya dafe rawaninsa ya zura a guje ya na faɗin, “Ka yi mini afuwa, ya kai Ifiritun Sulaimanu.”
Yayin da mutumin nan na cikin raga ya ga haka, sai ya ƙwala wa Masunci kira yana cewa, “Ya kai masunci, dawo ka fid da ni daga ragarka. Ni mutum ne irinka, kada ka gudu ka bar ni. Fitar da ni, na rantse da Allah zan saka maka da taimakon da ka yi mini.”
Yayin da Masunci ya ji haka, sai ya yi ƙarfin hali ya tsaya daga nesa, yana yi masa kallon raƙumin yara. Ya dubi mutumin da ke cukuikuye cikin raga ya tambaye shi, “Shin kai ba Ifiritu ba ne daga aljanu?”
Mutumin ya amsa masa, “Ni ba aljani ba ne, mutum ne irinka da ke rayuwa a ruwa. Kuma ni Musulmi ne, na yi imani da Allah da Ma’aikinsa.”
Masunci ya sake tambayarsa, “Wa ya jefa ka cikin ruwa?”
Mutumin ya amsa, “Ina daga cikin zuri’ar ‘yan ruwa. A ruwa Allah ya hallice mu, a nan muke rayuwa. Yanzu ma na fito yawo ne sai ka jefa raga bisa kaina ta cukuikuye ni. Ba don ina tsoron Allah ba da tuni na tsittsinka ragar na yi gaba. To amma ni Musulmi ne da na yi imani da ƙaddara, don haka na haƙura da abin da Allah ya ƙaddara a kaina. Yanzu idan ka fitar da ni, na zama bawanka, kai kuma ubangidana. Duk abin da kake so shi zan yi maka.”
Masunci dai ya yi tsaye daga inda yake, bai motsa ba, yana wasi-wasi a cikin ransa, ya gudu ne ko ya tsaya.
Da Ɗanruwa ya ga haka sai ya sake cewa, “Shin za ka kwance ni don girman Allah, mu ƙulla alkawarin zama abokai? Kullum ka kawo mini kwandon kayan marmari daga tudu irinsu inabi, tuffa, dabino, kankana da sauran kayan marmari, an ce kuna da su da yawa bisa doron ƙasa, mu kuwa ba mu da su a ruwa, sai ruɓaɓɓu da kuka watsar cikin ruwa muke tsinta muna ci. Idan ka kawo mini kayan marmarin na juye, ni kuma zan cika maka kwandonka da duwatsu masu daraja na ƙarƙashin teku, irinsu zinariya, lu’ulu’u, zabarjadi, yaƙutu da jauhari, muna da su cikin ruwa da yawa, ba abin da muke yi da su. Ka yarda da wannan sharaɗi, ya kai abokina?”
Masunci ya ce, “Kafin na amince da kai, tun da har ka ce kai Musulmi ne, to mu karanta Fatiha, mu roƙi Allah ya tsine wa duk wanda ya cuci wani tsakaninmu?”
Suka karanta Fatiha tare, suka shafa. Sannan Masunci ya yarda ya matsa kusa gare shi, ya fitar da shi daga cikin koma. Ya tambayi sunansa.
Ɗanruwa ya ce, “Sunana Abdullahi. Duk sa’adda ka zo nan, idan ba ka tarar da ni ba, ka ɗaga murya ka yi kira da ƙarfi, ‘Ina kake ne Abdullahi, ina kake ya kai Ɗanruwa?’ To duk inda nake a cikin ruwa, zan fito zuwa gare ka da hanzari.”
Za mu ci gaba, in sha Allah.
Marubuci:
Bukar Mada