HIKAYAR ABDULLAHI MASUNCI DA ABDULLAHI ƊANRUWA
Abdullahi ya kasance masunci, wanda yake da mata tasa ɗaya da ‘ya’ya tara. Ya kasance talaka, bai mallaki komai ba a duniya, face komarsa ta kamun kifi.
Kullum yakan tafi bakin teku ya jefa koma, idan ya kama kifi kaɗan sai ya sayar ya yi wa iyalinsa hidima da ‘yan kuɗin da Allah ya hore masa a wannan rana. Haka kuma idan ya kama kifi mai yawa sai ya sayar ya kashe kuɗin duka wajen sayen abinci da nama da kayan marmari iri-iri, ya kai gida su yi ta shagali da iyali. Shi bai san wani abu tanadi ba, yakan ce, “Abincin yau na yau ne, Allah shi ke ba da na gobe.”
Ana nan, ran nan, matarsa ta haihu. ‘Ya’yansa suka cika goma daidai. Sa’adda aka yi haihuwar kuwa ba shi da ko ƙwaya a gida. Matar ta ce, “Maigida, jeka ka samo mana abin da za mu ci.”
Mijin ya ce, “Yanzu kuwa, da yardar Ubangiji, zan tafi zuwa ga bahar in jefa komata, in nemo mana daga arzikin wannan yaro da aka haifa yanzu.”
Matar ta ce, “A’a maigida, kai dai nemo mana arziki daga taskar Ubangiji, domin shi ke ba da arziki ga wanda ya so.”
Abdullahi ya saɓa koma a kafaɗa ya nufi bakin teku. Da isarsa, ya warware ta ya watsa cikin ruwa yana cewa, “Ya Allah ba ni daga arzikin wannan jariri. Ba ni mai yawa, kada ka ba ni kaɗan!”
Ya jira zuwa wani lokaci sa’annan ya jawo koma zuwa tudu, ya same ta cike da yashi da tarkacen shara da hakukuwa da fasassun kasake, babu kifi ko ɗaya. Ya zubar da wannan, ya sake jefawa yana jira. Can ya kuma fitowa da ita, bai samu komai ba sai shara. Ya jefa karo na uku da na huɗu da na biyar, amma ko kwaɗo bai kama ba. Da ya ga haka, sai ya sake mashigi. Haka ya yi ta yi, daga wannan wuri zuwa wancan, har rana ta yi gora tana shirin faɗuwa, Allah bai nufe shi da kama kifi ko ɗaya ba.
Abin ya ba shi mamaki, gayar mamaki. Ya ce a cikin ransa, “A’aha, shin wannan jariri bai zo da arzikinsa ba ne?”
Can kuma sai ya ce, “Ba shi dai yiwuwa Allah ya halicci ɗan Adam ya bar shi haka nan, domin shi mai yawan baiwa ne mai yawan kyauta. Bakin duk da Allah ya tsaga kuwa sai ya ba shi abin da zai ci.”
Ya saɓa komarsa ya nufi gida cikin tsananin damuwa, yana tunanin abin da zai kai wa iyalinsa na abinci. Ya tuna matarsa da ya bari da ɗanyen jego babu abinci, ya kuma tuna kwanyamin ɗiyansa, me zai ce musu cikin dare idan yunwa ta fara dafa su? Yana tafe yana ta saƙe-saƙe cikin zuciyarsa har ya iso ga rumfar wani mutum da ke toya gurasa.
Rumfar ta cika da mutane an zagaye mai gurasa ana ta ciniki. Shekarar kuwa ta kasance ana ɗan mudu, abinci ya wuyata ga mutane. Akasarin waɗanda suka zagaye mai gurasar nan duk bashi suka zo nema, ga shi ya tara bashi mai yawa a hannun mutane, sun riƙe sun ƙi biya. Don haka ya ƙi kula kowa daga cikin waɗanda suka zagaye shi.
Masunci ya tsaya gaban rumfa yana kallon mutane, ƙamshin gurasa na jifarsa yana haɗiyar miyau, sai cikinsa ke kiran ciroma don yunwa. Can mai gurasa ya hange shi, ya kwala masa kira, “Taho nan, ya kai masunci!”
Abdullahi ya tafi gaban mai gurasa ya tsaya. Mutumin ya tambaye shi, “Kana buƙatar gurasa ne?”
Abdullahi ya yi shiru bai amsa ba.
Mai gurasa ya ce, “Yi magana mana, kada ka ji kunya. Idan ba ka da kuɗi zan ba ka bashi har sa’adda Allah ya hore maka, domin shi ne mai wadata bayi sadda ya so.”
Masunci ya nisa ya ce, “Wallahi ba ni da kuɗi, ya shugabana. Ga jinginar komata zuwa gobe, ka ba ni gurasar da zan kai wa iyalina.”
Mai gurasa ya yi dariya ya ce, “Wannan koma ai ita ce rumfarka, ita ce kuma ƙofar da abincinka na yau da kullum ke shigowa gare ka, idan na amshe ta da me za ka nemi abinci? Ta yaya kuma za ka biya ni? Kai dai faɗa mini ko gurasa ta nawa ke isarka.”
Masunci ya ce, “Ba ni ta rabin azurfa goma.”
Mai gurasa ya kawo gurasa ta nusufi goma ya ba masunci, ya kuma ƙirgo wasu nusufi goma na azurfa ya ba shi ya ce, “Karɓi wannan ka yi cefane. Idan Allah ya kai mu gobe, ka kawo mini kifi na nusufi ashirin. Idan ma ba ka kama kifin ba, ka dawo zan ƙara maka gurasa ta nusufi goma da wasu nusufi goma na cefane.
Marubuci:
Bukar Mada