Lallai ku sani wasu lokutan cutukan Bayi (Toilet) basu bayyana a jikin me dauke da su, wannan ne yasa idan mutum daya nada cutar har ta bayyana to wajibi ne suyi magani tare da duk wani wanda suke amfani da toilet daya ko saduwa. Wannan ne yasa ko hospital aka je to ana bukatar ma’aurata suyi magani tare ko ayi gwajin tare.
Cutukan Bayi (Toilet) na da yawa kamar yadda muka sani hatta cutar hanta ana iya dauka ta Bayi musamman wajen kissing ko sharing numfashi.
Cututtukan Da Akan Iya Ɗauka A Bayi (Toilet)
- CHLAMYDIA,
- GONORRHEA,
- SYPHILIS,
- TRICHOMONIASIS da
- HERPES. Da sauransu
Kadan Daga Cikin Binciken Da Akayi Akan Cutar Bayi (Toilet)
- Fesowar yan kuyas-kuyas din kuraje masu dandazo ko manya masu launin ja ko ruwan kasa masu ruwa ga azabar kaikayi a kowanne yanki na jiki wannan na nuni da inda cutar tafi kamawa a jiki musamman al’aura, dubura harshe leɓe, tafin hannu ko kafa ko tsakiyar baya wannan alamun cutukan bayi (Toilet) na HIV ko SYPHILIS ko herpes kenan.
- Yawan samun ciwuka a jiki su ki warkewa su gwambace musamman a ciki wanda ake kira ulcers, hakan na jawo wahala wajen fitsari ko yazo da jini ko mugunya me warin gaske. Ta waje ga mata suna samun gwambacewar farji ga maza gyambacewar hular azzakari ko harshe ko kumburin maraina ko kan azzakari ko farjin mace, wannan alamun SYPHILIS da HERPES kenan.
- Jin zafi a kwarkwaron azzakari ko jin zafi lokacin da fitsarin ke fita shima na daga alamun cutukan bayi (Toilet), wannan suna bangaren alamun cutukan mafitsara (UTI) ko duwatsun koda. Yin gwajin gaggawa a hospital kafin fara magani nada matukar amfani. Wannan alamun cutukan bayi (Toilet) ne masu suna CHLAMYDIA, GONORRHEA da HERPES kenan.
- Kumburewar al’aura da ba a saba gani ba akwai matsala sosai, kumburin na iya fitar da ruwa fari, ko me kauri ko me sirkin jini kuma da wari ko karni sosai wannan alamun cutukan bayi (Toilet) ne GONORRHEA, SYPHILIS ko CHLAMYDIA ne.
- Zubar jinin al’ada normal ne, amma yana fita da guda-guda da wari ko karnin gaske ko da sirkin ruwa bana dauraya ba shima akwai alamun cutukan bayi (Toilet). Ko al’ada tana wasa ko tana zuwa da matsanancin ciwon mara, alamun CHLAMYDIA ko GONORRHEA ne.
- Kaikayin jiki bana motsin gariza ba (allergy) kaikayin matse-matsi, azzakari, farji farko ko tsakiya, inda gashi yake fita daukewar sha’awa rashin kuzarin Azzakari wanda ba basur ya kawo ba gajarcewar al’aura mace ko na miji kaikayin dubura duk alamun cutukan bayi (Toilet) ne na CHLAMYDIA, GONORRHEA, TRICHOMONIASIS HERPES da WARTS.
- Yawan jin ciwon kasan ciki bangaren koda da hanta jin ciwo a kasan hakarkari alamu ne na cutukan bayi (Toilet) sun haura sun fara kama manyan gabobin jiki ayi gwajin hospital kafin fara magani nada matukar amfani.
- Yawan zazzabi alamu ne na jiki na kokarin yaki da kamuwa da wata cuta, wannan na iya zama alamun kamuwa da cutukan bayi (Toilet) kamar yadda wasu ke complain sunyi jima’i suna gamawa da kwana biyu ko daya ko awanni zazzabi ya rufe su da ciwon kai. Duka wadannan na bukatar dogon bincike da tambayoyi kafin bada magani.
- Yawan samun kumburin makoshi, hammata mara da sauransu ayi gaggawar gwaji dan alamun HIV, GONORRHEA SYPHILIS ne.
- Yawan zawo ko ciwon hanji me tsanani. Sau da yawa ana ganin zawo nada alaka da cin abinci mara kyau, to ku sani cutukan bayi (Toilet) na kawo irin wannan alamun.
Allah ya bamu lafiya da abun da lafiya za ta ci.
Daga Shafin:
SHIFA TRADITIONAL MEDICINE