Halima Ahmad Muhammad da akafi sani da Sadiya Kabala, an haife ta a ranar 27ga watan June na shekarar alif 1992 a garin Kaduna dake Najeriya.
Kabala Tayi Karatun ta na Firamare da sakandare duk a garin Kaduna, bata cigaba da karatu ba ta tsunduma harkar fina finan Hausa inda ta fara fim na farko mai suna Haidar a shekarar 2015.
Sadiya Kabala tayi wani fim mai suna Ƙorariya wanda Ali Nuhu ya shirya, fim ɗin da yasa tasamu ɗauka ka mai mutuƙar gaske wanda Kamfanin Shirya finafinai na FKD ya gabatar.
Sadiya Kabala bata daɗe cikin harka fina finan Hausa ba sai tayi Aure a garin Jos, Amma sai daga baya auren nata ya mutu. Anyi mata tayin ta dawo harkar fim amma ta nuna rashin yadda kasancewar lokacin hankalin ta bai karkata a harkar fim ba tafi sha’awar kasuwanci.
An tambayi Sadiya Kabala ko akwai wata kyauta data saka ta farin ciki?
Sai tace a rayuwar ta tana da burin zuwa aikin hajji Allah kuma cikin ikonsa sai akayi mata kyautar kujerar zuwa hajji, wadda ta ce hakan yaɗata farin ciki matuƙa a rayuwar ta.