Amfanin Bagaruwar Makka Ga Lafiyar Jikin Dan Adam

0 1,772

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Kadan daga cikin amfanin Bagaruwar Makkah su ne kamar haka:

1- Idan aka cire kwallon dabam akayi garinta ana sanya karamin cokali 3 a ruwan zafi kofi daya ana sha hakan yana magance matsalar Mafitsara, ciwon mara da sauran cututtukan dake damun mata. DA YARDAR ALLAH.

2- Idan aka hada garinta da garin Hulba ana zuba cokali 3( karami) a ruwan dumi kofi 1 ana sha kamar shayi, hakan yana magance matsalar ciwon Diabetics Kuma yana Kara ruwan nono ga masu shayarwa. Da YARDAR ALLAH.

3- Idan aka samu garinta da garin kwallonta aka hade su wuri guda ana sanya karamin cokali 3 a kofin ruwan dumi ana sha kamar shayi, hakan yana magance matsalar ciwon Uwar hanji, da ciwon Ulcer da kuma sauran cututtukan da suka shafi ciki, da Yardar ALLAH.

4- Idan mutum yana shan shayinta kuma yana cinta akai-akai, hakam yana wanke masa makogwaro, ya karawa mutum kyawun sauti kuma ya magance matsalar tari na yara da na manya.

Amma duk sai da izinin Allah.

Wanan kadan kenan daga cikin amfanin Bagaruwar Makkah.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »