MARINA CHAPMAN:
An haifi Marina Chapman a wajajen shekarar alib 1950, an kuma sace tana da shekaru Biyar 5 a duniya, ana zargin masu sace ta ne suka yanke shawarar barinta cikin wani babban jeji dake da dogwayen bishiyu a garin Kolanbiya.
Marina ta taso cikin manyan Cirai dake rayuwa cikin Dajin , har ta koyi ciyar da kanta da abincin da biran ke ci, taci gaba da rayuwa cikin manyan bishiyun da Biran ke rayuwa a ciki.
Marina na tafiya da kafa da hannu a lokaci guda kamar yada Birai keyi, kuma tana Magana da kara irin ta Biri.
Har ta taba bada labarin cewa akwai wani lokaci da rashin lafiya yayi Kamari a jikin wani babban Biri yay mata jagora zuwa wani tafkin Ruwa marar dadi tasha kuma ta samu lafiya.
Marina tasamu tsahon shekaru biyar tare da biran, lokacin da wasu mafarauta suka kubutar da ita daga wurin biran.
BELLO:
A shekarar alib 1996 wasu mafarauta suka gano Bello a cikin wata tawaga ta Birarrika a dajin Falgore dake Kano a Nijeriya a lokacin yana da shekaru biyu a duniya.
Ana zargin iyayen Bello da yar dashi yana da watanni shidda a duniya, kasancewar tawaya jikinsa.
Ansamu Bello da yin dabi’u irin na Biri har baya iya kwana a kan Gado sai dai kasa ko bishiya, sannan sannan baya iya Magana sai dai kara da ihu irin na Birrai.
OXANA MALAYA:
An haifeta a kasar Ukiren, ana zargin iyayenta da yin Shaye-shaye irin na giya suka yarda da ita tana da shekaru uku a duniya.
An tsinci Oxana cikin wasu manyan karnuka, tana haushi, cin abin ci da kuma lasar Jiki irin na Kare. Haka zalika Oxan na tafiya da hannu da kafa lokaci guda dabiu da duk wata rayuwar ta tana tin irin na Kare.
An tsinci Oxana lokacin da take da shekaru bakwai da rabi a duniya, an kaita gidan raino inda akayi ta kokarin koya mata Magana da dabiu irin na muta ne.
Anci nasarara koya mata wasu dabiun da muta ne keyi, amma likitoci sun tabbatar bazata taba dawowa kamar yadda dan Adam ke rayuwa ba.
DINA SANICHER:
An haifi Dina a wajajen shekara alib 1860 zuwa 1861. An tsince shi yana da shekaru shida a duniya a wani Jeji dake Indiya tare da karnukan daji.
Dina na tafiya da kafa da kuma hannu a lokaci, yana kuma cin danyen nama da tsotsar kasha sannan yana da dogwayen farata a hannu da kafa kuma yanada dogwayen hakora, yana rayuwa irin ta karnukan dake Jeji.
Sannan yana kara da ihu irin na Karnukan Daji, haka kuma idan aka bashi abinci saya sansana idan kamshin abincin yay masa yaci idan bai mas aba sai ya ture.
Mafarautan da suka kubutar dashi daga Karnukan Dajin ne suka saka masa suna Dina Sanicher.
An koyar da Dina rayuwa irin ta mutane har na tsahon shekaru ashirin (20) amma baya iya Magana saidai kara da ihu irin na karanukan Daji.
Ya rasu a shekarar alib 1895 sakamakon cutar shan taba.
JOHN SSBUNYA:
An haifeshi kasar Uganda, lokacin da yake da shekaru 4 zuwa 5 yaga mahaifinsa ya kasha mahaifiyarsa. A mai makon ya gudu cikin Jamaa sai ya shiga Jeji.
Birai ne Suka dauki John suka kuma cigaba da rainon sa har ya koyi har ya koyi tafitya da ihu irin na birai da kuma cin abincin su.
A shekarar alib 1991 aka kubutar dashi daga hannun Biran, kafin kubutar da john saida akayi fada sosai da Biran da suke tare da John.
An koyar dashi rayuwa irin ta mutane har yazama mawaki a kasar ta Uganda.
DANIEL:
A shekarar alib 1990 aka tsinci Daniel a wani Jeji dake Kasar Andes, Peru kasar dake Kudancin Amruka yana da shekaru 12 a duniya a cikin wasu garke na Akuyoyi.
An samu Daniel da cin ciyawa da kuma shan Nonan Akuya da kuma kuka irin na akuyoyi, sannan Daniel na tafiya da kafa da kuma hannu a lokaci guda.