Sanadin So (Kashi na 7 Hausa Novel)

0 129

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

SANADIN SO KASHI NA BAKWAI

Na ce da ita, cikin muryar rarrashi saboda gaba daya na gama tsinkewa da al’amarinta. Laifinka ne Darling saboda na fada maka ba zan iya rayuwa ba kai ba, na bukaci ka bari mu ci gaba da waya kuma mu dinga communicating a social network kamar da amma ka ki, na yi iya kokarina in ga cewar na fitar da kai cikin raina abu ya faskara.

Ta fada tana yi min fari da idanunta.
Amma kuma ai ya kamata ki san cewa cikin fushin ubangiji ne kike son jefani, ta yaya zan amince da wannan bukatar taki, kuma idan ma ban ji tsoron Allah ba ai ko don gudun azabar mijinki dole in kaurace maki. Na ce da ita Calm down mana Kudancy in dai matsalar mijina ce nayi maka alkawarin ba zai koma tabamin kai ba.

Tayi saurin katseni Wasa-wasa Fateema ta maida unguwarmu kamar gidansu kusan kullum sai ta zo wajena in bata zo gidanmu ba to zata sameni shago kuma kullum ta zo zancen daya ne, ba irin magiyar da ban yi mata ba akan ta daina zuwa wajena, sai cewa tayi idan ina so ta daina zuwa inda nake to in bari mu ci gaba da hulda a social network kamar yanda muke a da, tun abin baya damuna har ya fara damuna ga mutanen unguwarmu sun fara tsegumina,gidanmu kuwa mahaifiyata kullum sai tayi min fada akan yawan zuwan da Fateema ke yi nemana tun inai mata karyar dinki ne ke kawota har ta daina yarda da karyar.

Da na fahimci ba zata daina zuwa ba tilas na amince da bukatar. BABBAN GANGANCINA KENAN DANAYI
ARAYUWA. Amincewar da nayi wa fateema muka ci gaba da hulda a social network da kuma ta waya kamar da, ya sa ta daina zuwa unguwarmu.o  da yaushe sai dai mu rika haduwa af facebook ko WhatsApp, ko kuma ta kirani a waya Haka Al’amarin ya ci gaba da

 

kasancewa har zuwa wasu ‘yan kwanaki… Yau ma kamar kullum zaune nake a kan keken dinkina, ina dinki. Kamar daga sama nagansu, sun fado cikin shagon, basu tsaya cewa dani komai ba cakumoni kawai suka yi suka yi waje dani suka yi jifa dani cikin motarsu kirar Hilux, kamar fitar kibiya daga kwari, haka suka figi motar suka yi gaba dani.

Yaran Kwamanda ne (Sojoji) Tun cikin motar suka fara nukurkusata, koda muka isa barikin tuni na fice daga hayyacina. Koda hankalina ya dawo jikina, na ganni ne a wani daki da zan iya kira da kurkuku mafi kunci a duniya. Ba sai na tsaya wani bincike ba na san Kwamanda ne ya sa aka kamoni saboda kunnen uwar shegu da nayi da gargadinsa.


Nadama ce ta zomin irin wacce ban taba yinta a rayuwata ba tunanin wahalar da na sha kwanakin baya a hannunsa ta ya zomin, lokaci daya kuma tsanar fateema ta shigeni lokacin da na tuna da alkawarin da ta yi min a farkon zuwanta shagon dinkina.

Tabbas Fateema annoba ce a rayuwata… Karar bude dakin ce ta katseni daga tunanin da nake yi lokaci daya tsoro ya dabaibayeni na tsura wa kofar idanu, don ganin wa zai shigo.

Kwamanda ne ya shigo. Sanye yake cikin kaki (Uniform) ba kamar wancan karon ba, kallo daya nayi wa fuskarsa na fahimci ransa yayi mutukar baci. Kunnen kashi ne da kai ko yaro? Ya jefamin tambaya. Bai bani damar amsa masa tambayarsa ba kai tsaye ya ci gaba da magana.


Ko da yake laifina ne da na baka damar da zaka bijirewa umarnina, da na batar da kai tun a wancan lokacin da tuni nayi maganin taurin kan nan naka.

Amma ko yanzu ban makara ba, ina da damar yin hakan. Ban ankara ba sai ganinsa nayi rike da bindiga yana kokarin saita kokon kaina. Saboda firgici ban san lokacin da fitsari ya kubucemin a wando ba,..nan danan nahau addu’an daduk tafadomin abakina..tsawon minti 3 nadauka inajiran inji saukan bindigar akaina amma shiru


GUYS zamu ci gaba gobe a part 7 insha allahu
ME RA’AYINKU AKAN WANNAN LABARIN ???

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »