Takaitaccen Tarihin Kabiru Na Kwango.

1 709

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

KABIRU ABUBAKAR ALIYU wanda akafi sani da (KABIRU NA KONGO) An haife shi a shekarar alib 1962.

Kuma yayi karatu a hannun mahaifin sa sannan yayi karatu a hannun wani malaminsa mai suna Malanm Abu Zamzan Daganan ya wuce makarnat koyan Hrashen Larabci wanda a turance ake kira da school of Arabic Studies, wanda bai kai ga kammlata ba, ya shiga primary school domin yin ilimin boko a shekarar alib 1974 zuwa 1980, daganan ya shiga makarantar gaba da primary wato scondary school mai suna GOVERNMENT SECONDARY COMERCIAL a shekarar alib 1985.

Sannan yayi karatun NCE a shekarar alib 2001 zuwa 2004 a FCE KANO Sannan yayi Aure tun kafin yakai ga kammala Karantun sa na secondary school.

SHIGARSA HARKAR FILM
Ya tashi tun a yarintar sa mai sha’awar harkar film saidai kuma a wannan lokacin
bai sami damar shiga ba sakamakon mahaifin sa bazai barshi ba domin a wannan lokaci karatu ne mahaifin nasa yake son yayi,

A lokacin daya fara harkan wasan kwaikwayo, Lokacin da recoder ta shigo kasar hausa wacce ake iya daukan sound record suke amfani dashi wajen yin wasan kwaikwayo wanda ake sanyawa a gidan radio, Tare da wasu yan wasa irn su marigayi Hashem sa’ad, da marigayi Ibrahim Sulaiman, da sauran su, daga baya ya shiga kungiyoyi da dama da harkar wasan kwaiwayo, sun kafa wata kungiya maisuna SARDAUNA YOUTH AND DRAMATIC ASSOCIATION, wanda a cikin wannan kungiya yayi fice sosai, Ya kafa kungiya wanda ya jagoranceta mai suna DABO FILMS

Film dinsa na farko na video wanda ya bayyana mai suna KILU TAJA BAU na kamfanin hamisu iyantama

sannan ya bayyana a fina finai biyu da suka haskaka shi a duniya wanda tauraruwansa ta fara haskawa aka gane waye kabiru na kongo a cikin harkan film
LINZAMI DA WUTA, TAWAKKALI

Sannan a tattaunawan da aka yi dashi a A gidan Radiyo na BBCHAUSA ya bayyana abinda yake bata masa rai wanda yace:

“Bayason yaga ana rashin da’a a titi ko aikata wani abu wanda ya shafi rashin gaskiya da son zuciya hakan ba karamin bata masa rai yake yiba”.

Sanna ya bayyana abinda yake faranta masa rai wanda yace:

“Yana son yaga ana aikata gaskiya, sannan babban abinda yafi komai faranta masa rai yaji ransa yayi fari shine yazo yaji yara na karatun Alqur’ani hakan ba karamin faranta masa rai yake ba”.

Haka zalika akwai makaranta ta islamiyya wanda yake jagoranta da yake koyar da Alqur’ani mai girma da littafai ga al’ummar yankin sa.

Daga Bakin Mai Ita BBCHAUSA.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. ABDURRASHEED YAKUBU SHALL says

    MASHA ALLAH

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »