SANADIN SO KASHI NA DAYA
Karar shigowan sakon Whatsapp a wayata ne ya farkar dani daga baccin da ya fara daukata a kan keken dinkina. Kamar ba zan duba wayar ba, saboda idan da sabo na saba. kulli yaumin sakunan WhatsApp din basa rabo da zarya a wayata na mutane dabam- dabam a sassan kasar nan masu bibiyar
labaraina a facebook……
Idan na ce biye musu zanyi, ba barina zasu yi neman abin sawa a bakina ba, shi yasa a duk lokacin da nake a shagon dinkin bana kula sakunan.
Amma ga mamakina yau sai naji ina bukatar duba wayar in ga sakon waye ya shigo.
Kamar kullum yau ma bakuwar lamba naci karo da ita da gajeren sakonta na sallama.
Kamar ba zan amsa ba sai dai na daure na mayar da martanin sallamar. Wanda wanna shine farkon sanadin jefa kaina cikin wani mummunar hadari mtsww dana sani keyace…
Sakon lambar ya ci gaba da shigowa ABDULRAZAQ KUDANCY koh?
Eh! Da wa nake magana? Na bada amsa tare da yin tawa tambayar.
Fateema, daya daga cikin fans dinka a Dandalin facebook, aka bani amsa, naga wani post da kayi kwanakin baya, naji dadin post din shi yasa nace bari nayi adding dinka nan in nuna maka jin dadina. Allah Sarki! Wane post kenan? Na sake
tambayarta.
Post din Hasashe game da matsalolin maza, gaskiya naji dadin post din sosai, ta bani amsa. Na gode, kuma da yardar Allah zan ci gaba da yin wasu post din wadanda suka fi wannan dadi.
Allah ko? Gaskia ko KUDANCY idan ka ci gaba da nishandantar dani zan ji dadi sosai, saboda zaka sa ni manta da bakin cikin da ke damuwata.
Ke kuwa wane bakin ciki ne wannan? Na jefa mata tambaya cikin zakuwa da son jin damuwarta. Murmushi tayi gami da cewa kar ka damu idan lokaci yayi zaka sani.
Ba zan iya tantance dogon lokacin da na dauka ina hira da baiwar Allar nan ba, abinda kawai na sani a ranar bata barni nayi dinki ba har lokacin barina shagon yayi. Tunda daga wannan lokacin shakuwa mai karfi ta kullu tsakaninmu da fateema, duk yanda zanyi in samo labarin da zan tura mata wanda zai sakata nishadi sai nayi.
Wani lokacin idan labaran suka kakare min sai naji kamar na koyi halin hankakar da wasu ke yi a duniyar fesbuk akan labaran mutane, sai kuma in tuna da yanda zuciyata
ke tafasa a duk lokacin da naga wani ya satar min labari ya mayar da shi na sa, dole sai in fasa. Ranar da duk kuwa banyi postin labari ba ko na tura mata a WhatsApp ba ranar zan sha kiran wayarta, a duk lokacin da ta kirani na kan samu karyar da nayi mata.
A irin haka ne wata rana labaran suka kakare min, duk wata kafa da nake tunanin samun labari ta toshe na samu kusan kwana uku ba wani labari, sai ga kiran mutuniyar, bayanbmun gaisa, ta fara aikinta wato tambayata a kan na daina nishadantar da ita, rasa karyarda zan yi mata nayi saboda ban son fada mata cewa labaran ne babu, karya nayi mata cewa bani da data ne a wayata Suscribtion dina ya kare.
Har ga Allah na yi mata wannan karyar ne saboda bana tunani mace zata iya tura wa namiji kati babu wata alaka ta jini a tsakaninsu, amma ga mamakina bayan mun gama waya da ita kawai sai ga sakonta na tes ya shigo, ina dubawa lambobin kati na gani kasansu kuma tayi rubutu kamar haka:-
KUDANCY ga kati nan kayi maleji dashi 1500 ne ba yawa.
Ina gama karantawa kiranta nayi, tana dagawa nace Haba! Fateema ya zaki min haka? Gaskiya ki bar katinki bana so, ina da kudi zan saya da kaina.
Nayi juyin duniyar nan akan ta barshi ta kiya, da taga na matsa sai cemin tayi sai dai idan ban so kar in loda in bai wa wani don ita ta riga ta bani kuma na raina kyautarta ne shi yasa na ce ba na so, kuma ta gode. Da naga ta hasala dole na dawo
bata hakuri, da kyar ta sauko, sannan nayi mata godiya na kashe wayata. Ai kuwa tun daga ranar kati ya daina katsewa a wayata.
Idan har bani da kudi a wayar a kalla ka sameni da naira dubu ciki, ba kuma ni nake saya da kaina ba ita ce da take turomin.
DANA SANI KEYACE.
Wannan dalilin jefa kaina cikin wahala na yanka kazan wahala ma kaina kumana fige naci karoda wani babban dutsen daya fasan zuciya asanadin fateema…
Wannan fa..?
ZAMUCI GABA A part 2
Ab Kudancy