“Duk wata hanyar neman kariya ko neman tsari (wanda Allah ne kadai ke iya yinsa) da za a nema a wurin wanin Allah, to bin wannan hanyar Haramun ne kuma ya zama wajibi masu aikata hakan da wadanda ake aikatawa su tuba kafin mutuwa ta riske su ko kuma su mutu ba su da imani, a karshe kuma su hadu da azabar ALLAH. Allah ya kara tsare mana imaninmu.”
Malamar tace: Shari’ar Allah da hanyar ManzonSa Sallallahu alaihi Wasallama sun tarbiyyantar da mu akan cewa: Kar mu kuskura mu riki wani abu ko mu aikata wani abu ko mu maqala ko mu dogara ga wani abu da sunan neman tsari ko neman kariyar mu da na yaranmu daga sharrin halittun Allah, sai abinda Shari’ar ta fada mana kuma ta nuna mana shi sannan ta halasta mana shi ne kadai za muyi amfani da su.
Bareerah: Kai… Masha Allah, Amma gsky Ina jin dadin bayanin malamar nan, domin tana yin bayanin abinda ke damun Al’ummar mu ne a halin yanzu.
Labeeba: Ai ingaya miki yanzu ne ma nake ganin kamar za a fara karatun saboda ananne gizo ke yin saqarsa, domin yadda mata suke shige-shigen Malaman tsubbu da bokaye wai da sunan samun abinda suke kira wai kau-da-bara ko kariya musamman ma idan suna dauke da juna biyu.
Bareerah: Kaico…. Allah ya saukaka kuma yakara tsare mana imaninmu.
Malamar taci gaba da cewa: Amma maganar gsky babu wani abinda Shari’ar Allah da hanyar ManzonSA Sallallahu alaihi Wasallama suka nuna cewa mace mai ciki za ta rika maqalawa ko daurawa a ciki ko a jiki ko a qugu da sauransu, duk da sunan wai kariya ko neman tsari ga jaririn da suke dauke da shi.
Mai gabatarwa: To Malama kenan har wasu magungunan da mace mai ciki ke sha ko take shafawa a jikinta ko cikinta da zummar ALLAH yabaiwa cikinta kariyar da tsaro.
Malama: Ai bayan abinda ALLAH da ManzonSa Sallallahu alaihi Wasallama suka fadi, shari’a Kuma ta bayar da damar yin aiki da IJTIHADI, kamar mutum yayi bincike ya gano wani magani ko wani abu wanda ya halasta kuma bai saba ba ko baici karo da abinda Allah da ManzonSa Sallallahu alaihi Wasallama suka ce ba, wannan ba matsala za a iya amfani da shi ta hanyar da ta dace da shari’ar Muslunci.
Mai gabatarwa : To mallama kamar wadanne magungunan ne yakamata mai ciki tarika amfani da su domin samun kariyar Allah wa cikin da take dauke da shi.?
(Insha ALLAH a rubutu nagaba za muji irin magungunan da ya kamata.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin karin bayani:
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com