“Kambun-baka gaskiya ne domin yana faruwa kuma yana iya kai mutum ga mahallaka (mutuwa) saboda tsabar tasirinsa a jikin mutum, saboda haka ya zama wajibi mu nemi kariyar ALLAH Shi kaɗai, sai riko da hanyoyin samun waraka ko riga-kafi wadanda suka inganta a shari’ar Allah wajan kare kanmu da iyalanmu daga sharrin Kambun-baka da hassada.”
Bareerah na ganin takardar gayyatar sai tace: Alhamdulillah amma gaskiya wannan muhadarar da za ayi magana akan KAMBUN-BAKA da HASSADA za ta kayatar da al’umma matukar gaske domin halin da ake ciki kenan a wannan zamanin, sai kaga yaro yayi ta fama da rashin lafiyar da ake rasa gane kanta, ko kuma yaro ya taso da hazaqa, kokari, kuzari, azama, k’wazo da kuma basira amma daga baya sai kaga ya lamarin ya lalace.
Labeeba: Lallaikam, ai nima insha Allah har makobtanmu zan gayyata suzo suji wannan fadakarwar domin a gudu tare kuma a tsira tare.
Matar nan dai itama tace: Ai nima insha ALLAH ba bari na za ayi a baya ba, har da ni za ayi wannan muhadarar kuma zan gayyaci mutane domin su ma su amfana da fadakarwar.
Bareerah: Lallaikam wannan dabarar gayyato wasu da kukeyi ba karamin taimakawa mutane za tayi ba, saboda da yawa mutane muna sakaci wajan kiyayewa.
Matar dai tayi musu tambaya tana cewa: Shin ni yanzu ya za muyi ne da yar uwata din da ta dade bata samu mijin aure ba?
Bareerah: ALLAH Sarki, ai ‘yar uwa nutsuwa yakamata kuyi kuma kudaina matsa mata akan lallai ilalla sai ta samo mijin aure ta ko wane hali, kwantar mata da hankali za ku rika yi kuna nuna mata cewa komai lokaci ne kuma ALLAH yana sane da dukkanin halin da take ciki .
Labeeba: Sannan kuma ya kamata kufahimci cewa : Ba yin kanta bane, saboda duk wanda ta rasa to ba rabonta bane amma idan rabonta ne cikin k’addarawar ALLAH za ku ganshi ya dawo, kuma da zarar lokacin da ALLAH ya k’addara ya yi sai kuga wani sababin ya faru sai tayi aurenta ba tare da wata matsala ba, hakuri wajan bin shari’ar ALLAH dai shi ne abin bukata.
Bareerah: Kwarai kuwa yar uwa, ke dai abinda za mu kara jaddada muku shi anan shi ne: Ko kusa kar ku kuskura kuce za kuje wurin yan bori, boka ko kuma malaman tsubbu nemar mata maganin farin jini ko na samun miji, saboda ananne za ku rasa imaninku, ku sanya mata rashin kwanciyar hankali a rayuwaeta gaba daya, kuma a karshe sai ku kasance cikin hasararru matuƙar baku tuba ba.
Matar tayi farin ciki da godiya sosai tare da yi musu Addu’ar Allah yasaka da mafificin Alkhairi a bisa wayar da ita da sukayi game da tsayawa akan Tauhidi.
(Insha ALLAH za muji ci gaban lamarin a rubutu nagaba.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com