Alamomin Gidan Da Yake Dauke Da Kambun-baka Ko Hassada

0 180

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

1- Yawaitar samun matsaloli musamman ma tsakanin ma’aurata akan wasu dalilan da basu kai sun kawo ba, ta yadda za a rika dagawa juna murya ga rashin baiwa juna uzuri.

2- Yawan jin tsoro kuma mutum ya rika jin gidan ya gundure shi haka kurum.

3- Yawaitar samun damuwa da labarai na firgitarwa da rashin nutsuwa.

4- Yawaitar samun rashe-rashen lafiya iri-iri daga wannan sai wannan har su fara shan hankalin mutum.

5- Bayyanar wani wari a cikin gidan duk da kuwa ana tsaftace shi kuma komai turaren da aka sanya a gidan sai warin ya bayyana.

6- Tsagewar ban mamaki da bangwayen gidan za su rika yi.

7- Yaduwar Kwãri (musamman tururuwa) nan da nan sun mamaye ko ina a gidan, duk maganin da aka sanya musu kuwa ba sa guduwa.

8- Yawaitar samun gobara a gidan, nan da nan sai ayi gobara wani lokacin ma a rasa dalili.

9- Yawaitar bace-bacen abu a gidan ko da kuwa an kulle wurin ajiyar amma sai dai azo aga babu wani abu kuma ba tare da wata alamar an balle ba.

10- Yawaitar siyan abubuwa marasa amfani ko kaga dukiya ana kashe ta ta hanyar da ba ta dace ba, kuma karasa inda dukiyarka take tafiya ko kaga kasuwancin ka ya dagule.

MAFITA:

  • A dage wujan kiyaye dokokin Allah da cika salloli akan lokutansu.
  • A dage da yawaita karantawa ko sauraren Suratul Baqara a cikin gidan a ko da yaushe .
  • -A rika yawaita kunna kiran sallah a cikin gidan.
  • A rika yin nafulfulin dare ko na yini a gidan .
  • -Idan za a ajiye komai a gidan a rika fadin: “BISMILLAHI” kafin a ajiye shi.
  • Idan za a rufe kofa ko wani abin da za a rufe a gidan a rika fadin : “BISMILLAHI”.
  • A rika yin Azkaar na safiya da maraice da na ko da yaushe, musamman ma karanta Atmyatul Kursiyyu, Ikhlas, Falaqi da Naasi a bayan kowacce sallar farillah.
  • A rika tsaftace gidan a ko da yaushe ana sanya turare tare da kawar da yanar gizo-gizo a kowane sako da lungunan gidan.

Sai kuma ayi riko da wasu sabubba wadanda basu sabawa Shari’ar Allah ba, insha Allah za a dace cikin hukuncin Allah.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »