Ummu Labeeba ta amsa da cewa: Aameen ya Rabb.
Ummu Arqam: Ke dai na yiwa Abu Arqam maganar mai maganin nan, kuma ya bani kwarin gwiwa amma dai ya ce zai fara tuntubar Abu Labeeba tukunna.
Ummu Labeeba : Masha Allah, Allah yasa mudace Ameen. Kinga kuwa yanzu nima na kammala labartawa Abu Labeeba bayanin zuwanki da duk abinda muka tattauna da ke, sai ya fita yace min yanzu kuwa zaije wajan Abu Ruwaihah din .
Shi ma Abu Arqam yana kan hanyarsa ta zuwa gidan Abu Labeeba din kenan sai suka hadu a hanya.
Bayan sun gaisa ne sai Abu Labeeba yake cewa: Abu Arqam ina za ka ne haka cikin sauri kuma a wannan lokacin?
Cikin murmushi Abu Arqam ya amsa da cewa: Ina kuwa za ni inba wurinka ba, da ma akan wata magana ce da iyali na tace sun tattauna da iyalinka game da batun wani mai magani.
Abu Labeeba: Eh kwarai kuwa anyi haka, domin yanzu ma ina kan hanya ta ne ta zuwa wurin shi Abu Ruwaihah mai maganin.
Abu Arqam: Faduwa ta zo daidai da zama kenan. Amma ni gskiya Abu Labeeba abin bai gama Kwanta min a rai bane wallahi saboda har yanzu gani nakeyi ne kamar muna nuna rashin yarda da hukuncin da ALLAH yayi akanmu, kuma naga ai ita haihuwar nan Allah ne kadai ke bayar da ita, munje asibiti duk an duba mu an tabbatar kowa lafiya yake babu mai wata matsala a zahiri, kawai ni abinda naga ya fiye mana shi ne mu zubawa Sarautar ALLAH ido, amma ita Ummu Arqam ba ta ganewa game da wannan batun.
Abu Labeeba : ALLAH Sarki Dan uwa, tabbas Allah ne kadai ke iya bayar da haihuwa ga wanda yaga dama kuma ya hana haihuwar ga wanda yaga dama. Kuma ba wai ganewa ne batayi ba, ta gane kawai dai inajin ko tsaigumi, tsana da kananan maganganun da take ji ne a wajan mata yan uwanta ko kuma danginka suke neman yin tasiri a ziciyarta.
“Haka wasu ke dorawa zuciyarsu damuwa game da surutan mutane akan wai sunki haihuwa har hakan ya rika sanya su shiga wani hali ko yanayi na damuwa ta yadda suke kokarin jefa kansu cikin halaka suke su rasa imaninsu. Kar ku damu saboda Ubangijinku SHI ne ALLAH mai share hawayen duk wanda yake kyautata masa zato a dukkanin lamurransa.” (Insha ALLAHu za muji ci gaban tattaunawar a rubutu nagaba) Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba. (Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA) Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
ABIN LURA
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com