Abu Arqam: Eh kuma fa da alamar hakan, amma dai ni gaskiya dangina ba sa tsangamar Ummu Arqam akan rashin haihuwa, domin har yaba musu ma take yi wallahy saboda suna kyautata mata sosai, sai dai ko yan waje saboda komai za ai iya faruwa.
Abu Labeeba: Kwarai kuwa lallaikam ta yi dacen surukai Allah yakara zumunci, ina ma a ce sauran surukai za su zama kamar surukan Ummu Arqam wajan daina tsangwamarta saboda rashin haihuwa, ai ko da an zauna lafiya kuma da kowacce mace ta ji dadi hankalinta ya rika kwanciya, tunda dai haihuwar nan ALLAH ne mai bayarwa ba mutum ba.
Abu Labeeba yaci gaba da cewa: Amma shawarar da zan baka anan shi ne kayi kokari kayi riko da sabubban nan kuma kayiwa ALLAH kyakkyawan zato sannan kasanyawa zuciyarka yaqinin Allah ya ji kukan ka kuma da sannu zai share maka hawayenka ko badade ko bajima cikin IkonSA.
Abu Arqam: Alhamdulillah, ai Abu Labeeba wannan kullum zuciyata a cike take da kyautatawa ALLAH zato kuma Insha ALLAHu ina da yaqinin wannan lamarin zai zo karshe, tunda dai na tabbata SHI ne mai bayarwa kuma mai hanawa.
Abu Labeeba: Alhamdulillah ai haka akeso, ka ga sai mu karasa wajan Abu Ruwaihah din ko?
Abu Arqam: Abu Labeeba wato kar kaga ina ta jan wannan lamarin haka kayi tunanin wani abu dabam…. Kawai ni zuciyata ce har yanzu bata gama nutsuwa ba akan lamarin, amma dai yanzu shi mutumin nan ya yanayin maganinsa din yake ne ?
Abu Labeeba: ALLAH Sarki Dan uwa, ai nima yadda kake haka din nan wallahy burgeni kake yi sosai saboda yana da kyau mutum yakasance mai taka tsantsan a wajan neman magani musamman ma game sa abinda ya shafi haihuwa da neman Aure, domin ana batar da mutane da dama a wannan hanyar wallahi.
Abu Arqam: Yauwa Dan uwa, nima abinda nake gudu kenan wallahy.
Abu Labeeba: Na’am, wato gakiya dai shi wannan mutumin ba ya shirka kuma ba wai maganin haihuwa yake bayarwa ba a’a, saboda babu mai bayarwa kuma mai hanawa sai ALLAH, kawai shi Abu Ruwaihah matsalar zai fahimta ne matukar likitoci sun auna kuma sun tabbatar ba abinda ke damunku wanda zai iya yin sanadin hana ku haihuwar to sai yayi muku wasu tambayoyi.
Abu Arqam: Na’am, kamar wadanne tambayoyin kenan kuma akan wane abu ne za ayi tambayoyin?
(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji wadanne irin tambayoyi ne Abu Ruwaihah ke yiwa mutane.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com