Tarihin Marigayi Sarkin Zazzau Shehu Idris

0 770

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

An haifi Shehu Idris a ranar 20 ga watan Fabrairu shekarar alif 1936, malami ne kuma shine Sarkin Zazzau na 18,

Kafin zamansa Sarki ya zama shugaban majalisar masarautar Zazzau da majalisar sarakunan jihar Kaduna. Ya hau karagar mulki a ranar 8 ga watan Fabrairun shekarar alif 1975 bayan rasuwar Alhaji Muhammadu Aminu.

Idris shi ne sarki mafi dadewa a tarihin masarautar Zazzau, inda ya yi sarauta na tsawon shekaru 45 tun daga shekarar alif 1975 zuwa 2020. Ahmed Nuhu Bamalli ya gaje shi a matsayin Sarkin Zazzau na 19.

An haifi Shehu Idris a gidan Maiunguwa Idrisu Auta hakimin Unguwar Iya wanda ke tsakanin Unguwar Durumi da Kuyanbana a Masarautar Zazzau, ana kiran mahaifinsa Autan Sambo, mahaifiyarsa kuma ana kiranta Hajiya Aminatu.

Mahaifinsa Maiunguwa Idris ana yi masa laƙabi da Auta domin shi ne na ƙarshe a wajen Sarkin Zazzau Muhammadu Sambo wanda ya yi sarauta daga shekarar alif 1879 zuwa 1888, sarki Muhammadu Sambo shi ne ɗa na biyu ga Sarkin Zazzau Abdulkarimi wanda ya yi sarauta a shekarar alif ta 1834 zuwa 1846, don haka mahaifinsa ya kasance Hakimin Unguwa yayin da Kakansa suka kasance sarakuna a Masarautar Zazzau.

Idris ya fara karatunsa ne a garin Zariya wasu malaman addinin musulunci guda biyu suka ba shi horo sannan ya ci gaba da karatun boko a makarantar Elementary dake Zariya.

Ya kasance a makarantar firamare ta Elementary daga shekarar alif 1947 zuwa 1950, a lokacin ya rasa mahaifinsa yana dan shekara 12.

Idris ya ci gaba da karatun kur’ani da na boko sannan ya shiga makarantar Middle ta Zariya a shekarar alif 1950 kuma ya kammala karatu a shekarar alif 1955. Daga nan ya halarci kwalejin horar da malamai ta Katsina.

A shekarar alif 1958 ya zama malami a wata makaranta da ke Hunkuyi sannan kuma ya koyar a wasu ‘yan makarantu da ke Zariya.

A cikin shekarun alif 1960 ya zama sakataren na marigayi Sarkin Zazzau Muhammadu Aminu, sannan kuma an nada shi a matsayin sakataren majalisar masarautar Zariya a shekarar alif 1965.

A shekarar alif 1973 aka ba shi mukamin Dan Madamin Zariya kuma aka nada shi hakimin Zariya.

Idris ya gaji sarki Aminu ne bayan rasuwarsa a shekarar alif 1975. A ranar 10 ga watan Janairu, 2015 ya yi bikin cika shekaru 40 da nadin sarauta, kuma a ranar 8 ga watan Fabrairu 2020 ya yi bikin cika shekaru 45 da nadin sarauta.

Idris ya rasu ne da misalin karfe 11:00 na safe, a ranar 20 ga watan Satumba, 2020, a asibitin sojojin Najeriya da ke Kaduna. Allah ya jikansa, yasa Aljannah makomarsa Amin.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »