Northern People’s Congress (NPC) jam’iyyar siyasa ce a Najeriya. An kafa jam’iyyar a watan Yuni shekarar alif 1949, ta yi gagarumin tasiri a yankin Arewa tun daga shekarar alif 1950 har zuwa juyin mulkin soja a shekarar alif 1966. Ita ce ƙungiyar al’adu a da, da aka fi sani da Jamiyar Mutanem Arewa.
Bayan yaƙin basasar Najeriya na shekarar alif 1967, daga baya NPC ta zama koma baya a jam’iyun sisar Najeriya.
Shugaban wannan jam’iyya shi ne Sardaunan Sakkwato wanda kuma shi ne Firimiya na yankin Arewa, sannan kuma sai Sir Ahmadu Bello. Sir Alhaji Abubakar Tafawa Balewa mataimakin shugaban jam’iyyar kuma firaministan Najeriya.
Sun samar da Firayim Minista na farko wanda aka ƙirƙiri ofishinsa a shekarar alif 1957, kuma ya yi mulki a cikin jamhuriya ta farko daga shekarar alif 1963 zuwa 1966.
Daga baya dan jam’iyyar Makaman Bida ya zama shugaban jam’iyyar National Party of Nigeria a shekarar 1978. S. A. Ajayi ɗan jam’iyya shi ne shugaban NPC na jihar Kwara, tsohon sakataren majalisar Sardaunan Sakkwato.