Bayan Abu Labeeba ya kammala bayaninsa ne sai yace da Ummu Labeeba:
To ni dai zan tafi masallaci kinji an kira sallah. Amma don Allah idan Labeeba ta tashi a tabbatar ta yi alwala kuma ta yi sallah sannan tayi karatun Alqur’ani ko da shafi 1 ne.
Ummu Labeeba: ALLAH Sarki ai kuwa Insha ALLAHu zan sanyata tayi yadda kace din, duk da dai ai Labeeba ma ba da bam rashin lafiyar nan nata ba ai ba ranar da zata zo batayi abubuwan nan ba da kace, ai kaima nasan sheda ne akan hakan.
Abu Labeeba: Lallaikam nima na shaida hakan, ai ina gaya miki alakarta da Alqur’ani da kuma Azkaar ne yasa ma lamarin ke zuwa mata da sauki ba kamar na wasu ba kam.
Ummu Labeeba: Kwarai kuwa Abu Labeeba, ai wannan lamarin a bayyane yake domin duk wanda ya rike yawaita karatu da suararon Alqur’ani da kuma yin Azkaar a ko da yaushe to shi ne ya rike Ingantacciyar kariya domin ya nuna yan tare da Allah, sai kaga SHI ma ALLAH ya kasance tare da shi wajan bashi kariya.
Ummu Labeeba ta fuskanci Abu Labeeba tace masa: Insha ALLAHu zan aikata duk abinda kace idan Labeeba ta tashi daga baccinta, amma yanzu ga buta kayi alwalarka anan sai kaje masallacin don na ga yanzu an kusa tayar da Sallah, gwara ka samu ladan alwala a gida kuma dai ka samu darajar sahun farko ko na gaba.
Abu Labeeba yayiwa Ummu Labeeba godiya tare da Addu’ar Allah yasa tagama lafiya, sai ya wuce masallacin.
Bayan kwana biyu ne Labeeba ta shirya tafiya zuwa makaranta, sai ta hau NAPEP zuwa makarantar a cikin NAPEP din sai ta ga wata budurwa kamar ta santa sai tayi mata sallama.
Budurwar ta amsa sai Labeeba take ce mata: Baiwar naga kamar kina kama da wata mai suna HUDA wacce muka hadu a wajan wani mai magani ko?
Huda : ALLAHu Akbar ! Ba shakka kuwa nice Yar uwa, nima kuma kinga ai sai yanzu ma na fahimceki kuwa.
Suka sake wata gaisuwar ta musamman cikin farin ciki, sai Huda take cewa: To yar uwa ya jikin na ki ne ?
Labeeba: Alhamdulillah da sauki Gaskiya don na samu lafiya ba kamar farkon nan ba kam.
Huda : Alhamdulillah, nima kinga har na warke gaba daya kuma na samu na yi Aure tun watanni uku da suka shude.
Labeeba ta rungume Huda cikin mamaki da murmushi mai cike da farin ciki take cewa: Alhamdulillah Masha Allah ! gaskiya na yi miki murna sosai yar uwa Allah baku zaman lafiya, mu ma sai atayamu da Addu’a saboda mu ma ALLAH yabamu miji nagari.
Huda : Ameen ya Rabb, ALLAH ya aurar da ke ga miji nagari ke da sauran yan uwa masu bukatar aure. Ameen.
Labeeba ta amsa da cewa Aameen ya Hayyu ya Qayyum… Amma fa na yi mamakin ki wallahi.
Huda : Mamakin me kuma yar uwa?
Labeeba: Na ga lokacin da muka hadu ma ai an kusa auren naki kenan amma shi ne ko ki sanar da ni cewa an kusa aurenki ki gayyace ni natayaki murna !
Huda: Allah Sarki yar uwa, ai kinsan lokacin farkon haduwarmu ce, kuma ni tun ina karama Ummar mu tana fada mana cewa: Mu daina bayyana sirrukanmu ga bakin fuskoki wadanda bamu sani ba ko ma ga wadanda muka sani ne ba kowa za mu rika fadawa komai ba kuma ba komai ne za mu rika fadi ba.
Labeeba tayi shiru tana mamaki sai cewa tayi: Ikon ALLAH, kenan yin hakan ma wata dabara ce ko kuwa dai kawai salo ne na basaja da bazata ?
Huda: Ai bayan Umma tana fada mana haka kuma ina sauraron malamai musamman ma a Tafseerin nan na azumin bana suna ta fadakarwa akan cewa: Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu : Mu rika boye neman bukatocinmu dai dai kawai aga munayi ko munyi saboda gudun sharrin masu hassada da masu kambun-baka.
Labeeba ta kurawa Huda ido cikin mamaki tana cewa: Wato, kenan su Yan hassada da masu kanbun-baka din za su iya hana ruwa gudu ne ?
Huda tayi murmushi sai cewa tayi: Kwarai kuwa, ai sharrin Mahassada da masu kanbun-baka ba karami bane, tunda kinga ALLAH har saukar da Ayoyi yayi domin a rika neman tsari daga sharrin su.
Labeeba: Wato bayanin nan naki ya rikita ni sosai wallahi domin ina jin hakan yana cikin matsalar da nake fuskanta nima kaina.
(Insha ALLAHu kuwa za muji bayani a rubutu nagaba)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.)
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com