Abu Labeeba yayi mamaki sai cewa yayi: Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un ! Kai jama’a wato mallam shi yasa fa Al’ummar mu ke cikin rikici da matsalolin da muke rasa gane kansu.
Mai magani: Kuma fa ba iya nan ba, wato yanzu ma hatta idan mace tana da ciki sai kaga tun cikin na dan wata 3 ko 4 zuwa sama sai kaga tana bayyanawa duniya ai tana da ciki ta hanyar sanar da kawayenta ko kuma kaga ta dau hotonta da ke da alamar cikin ya fito ta sanya a social media wai tana neman Addu’a.
Abu Labeeba: Kai jama’a ka ji wani sakarcin kuma…. Wai ina muke so mu jefa rayuwar mu ne haka, abinda ake so a rika boyewa ana haba-haba da shi kar ma asan da akwai shi saboda magauta, har sai idan ya kai minzalin da zai bayyanar da kansa.
Mai magani :Ai kai ne kake da irin wannan tunanin haka, amma wasu ma mazajensu ne ke yin hakan.
Abu Labeeba: Ai kam ka ga dole shedanu su aboci al’ummar da ke aikata irin hakan, wacce ba ta iya boye sirrinta, bayan kuma Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ya yi mana umarni da mu rika boye neman mu har sai Allah ya bayyanashi ga mutane.
Mai magani: Ai ingaya maka wasu a garin nune-nunen da sukeyiwa duniya a social media musamman ma akan status dinsu, za kaga yan kambun baka na shafar cikin, ko kaga cikin ya zube tun bai kai inda yakai ba, ko kuma ya samu matsala ko dai kuma a haifi jaririn a wani irin matsanancin rashin lafiyar da ake rasa gane kansa.
Lamarin ya batawa Abu Labeeba Rai sosai yace: Kaicoo…. ALLAH yasa mudace kuma ya kyautata mana. Wato yadda na fahimta shi ne: Da ace za mu bi tsarin Addini yadda yakamata da kuwa babu wani shedanin da zai iya wahalar da mu balle har ya cutar da mu.
Mai magani: Tabbas kuwa… Ai riko da dokokin ALLAH shi ne maganin Wayyo ALLAH.
Mai magani ya baiwa labeeba magungunan da za ta rika amfani da su, yace nan da sati 1 su dawo domin kara jin yanayin jikin.
Abu Labeeba suka kama hanya suka nufi gida, ashe kuwa ita Salaha tuni har ta je wurin Ummu Labeeba tana tambayar ta tana cewa:
“Wai ina yarinyar ne, ko dai baki kammala shawarwarin naki bane na zuwa wurin mai maganin da na ba ki labarinta ba?”
Ummu Labeeba: Hmm ai dama na gaya miki Abbanta ba lallai ne ya amince ba, saboda Ni na rasa irin tsananin nan da yake da shi na gaira dalili .
Salaha: Kar dai ace wurin mai maganin da suke son zuwa suka je ?
Ummu Labeeba: Hmmm ai kema kinsan can zuciyarsa take sun zuwa.
Salaha: Hmmm, Lallaikam za a dade yarinyar nan bata warke ba kuwa, ga wurin mai magani nan kamar yankan wuka, su kuma sun tashi sunje wajan masu jiran Allah yayi ikonsa ! Ai bata lokacin su kawai za suyi.
“Kaicooo..Wato ita Salaha ta manta cewa, riko da sababin da shari’a tayi umarni da kuma dogara ga Allah, su kadai ne ingantacciyar hanyar samun waraka, saboda magani da mai magani wannan ba abinda za su iya bayarwa na waraka, dole sai an jira ALLAH ya yi ikonSA, saboda bai bar waraka a hannun kowa ba sai a hannunSA shi kaɗai Gwani mai bayar da lafiya da waraka.”
Ummu Labeeba : To… kinji dai ….Amma wannan kuma su ya shafa don ni abin ya fara isata gaskiya.
Suna cikin tattaunawar kenan sai ga Abu Labeeba da Labeeba sun karaso kofar gida, kafin suyi sallama sai Labeeba taji muryar Salaha, ta tsayar da Abbanta take ce masa:
” Abba wallahy ya kamata ka raba wannan matar da zuwa gidan nan domin ba karamin tashin hankali take son haifarwa a gidan nan ba, domin ita Umma na fahimci tana yarda da duk abinda take bata shawara akai kuma duk babu Alkhairi a cikin shawarwarin da take bata.”
Abu Labeeba: Eh lallaikam Labeeba kinyi tunani mai kyau kuma Allah yasaka miki da alkhairi, ya yiwa rayuwarki albarka, tabbas sai an tashi tsaye game da lamarin nan, Insha ALLAHu kuma zan yi iya bakin kokarina akan hakan.
Bayan Abu Labeeba ya yi sallama sai ya shiga gidan kai tsaye… Ummu Labeeba ta amsa sallamar.
Ita kuwa Salaha ta kasa nutsuwa, a tsorace dai suka gaisa da Abu Labeeba, a firgice ta kwashe tabarmar kunyarta ta fice daga gidan.
Abu Labeeba ya shige cikin daki, Ummu Labeeba ta biyo su a baya, yayi mata bayanin yadda lamarin yakasance a wurin mai maganin tare da maganin da ya basu da kuma yadda za ayi amfani da su, saboda haka sai a kiyaye.
Abu Labeeba yace da Labeeba: Dan bamu wuri za mu tattauna da ummanki, Labeeba kuwa ta mike ta fita waje.
“Haka akeso idan mai gida zaiyiwa matarsa fada ko nasiha akan wani kuskure da tayi, to kar ya yi a gaban yaransu, saboda kare mutuncin ita mahaifiyar a idanuwan yaran kuma hakan zai sa ta karbi nasihar hannu bibbiyu, amma idan a gaban yaran ne ba lallai shedan ya barta ta amsa laifinta ba.”
(Insha ALLAHu a rubutu na gaba za muji ci gaban bayanin.)
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com