Tsohon Fira Ministan Burtaniya, Winston Churchill, ya taba cewa: “Na hau tasi wata rana zuwa ofishin BBC don yin hira.
Da na isa, na ce direban ya jira ni na tsawon mintuna arba’in har sai na dawo, amma direban ya nemi gafara ya ce, “Ba zan iya ba, domin dole ne in koma gida in saurari jawabin Winston Churchill.”
Na yi mamaki kuma na yi farin ciki da sha’awar da mutumin ya nuna don sauraron jawabina! Sai na ciro fam goma na ba direban tasi ɗin ba tare da na fada masa ko ni wane ne ba. Sa’ad da direban ya karɓi kuɗin, ya ce: “Zan jira sa’o’i har na sama da minti sittin har sai ka dawo yallabai na fasa jin jawabin nasa. !”
Winston Churchill yace Kuna iya ganin yadda kuɗi kan gyara ƙa’idodi da ra’ayoyin mutane; ta haka ake sayar da al’ummai da kuɗi; mutane kan girmamawa ga kudi; iyalai su rabu don kuɗi; abokai sun rabu don kuɗi; ana kashe mutane don kuɗi, ana mayar da mutane bayi saboda kuɗi.
Abin Lura:
Wannan yana nuni da yadda zuciya ɗan adam ke makan cewa saboda kuɗi Ya Allah ƙasa nufi karfin zuciyar mu.