Aminu Sule Garo (an haife shi a shekara ta 1962) ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa. An zabe shi Sanata mai wakiltar Kano ta Arewa a watan Afrilun 2007, amma an soke zabensa a watan Disambar 2007 bisa ga rashin cancantar da ake bukatarsa dashi.
An haifi Aminu Sule Garo a garin Garo da ke karamar hukumar Kabo a jihar Kano a Najeriya a shekarar alif 1962. Mahaifinsa hamshakin dan kasuwa ne marigayi Alhaji Sule Galadima Garo.
Ya halarci kwalejin fasaha ta Wudil inda ya yi karatun sakandire, ya kuma zabi bai ci gaba da karatu mai zurfi ba don komawa kasuwanci.
Ya fara kasuwanci a matsayin darakta a Sule Galadima & Sons Limited, inda ya tashi ya zama shugaba kuma babban jami’in kamfanin Amaco Galadima Nigeria Limited.
Ya kasance shugaban kamfanin zuba jari na jihar Kano har sai da ya yi murabus a shekarar 2006 saboda burinsa na zama Sanata. Ya kuma zauna a kwamitin kamfanoni da dama, daya daga cikinsu shi ne Ja’iz International PLC.
Aminu Sule Garo Musulmi ne kuma ya auri Fatima (balaraba) wacce jikar Marigayi Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Yana da ‘ya’ya hudu.
SIYASA
An zabi Garo a matsayin dan majalisar wakilai daga 1992 zuwa 1993 da kuma daga 1995 zuwa 1996, yana wakiltar mazabar Kabo/Gwarzo a lokacin shugabancin Janar Ibrahim Babangida da Sani Abacha.
A watan Fabrairun shekarar 2007 ne aka gayyaci Aminu Sule Garo ya gurfana gaban kwamitin binciken gwamnatin tarayya kan zargin almundahana. A watan Afrilun 2007 ne aka zabe shi a matsayin dan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa a jam’iyyar ANPP.
A cikin watan Disamba na wannan shekarar, biyo bayan kalubalantar dan takarar jam’iyyar PDP, Sanata Bello Hayatu Gwarzo, an soke zabensa ne saboda rashin cancantar neman ilimi, Hayatu ya maye gurbinsa.