Tarihin Sheikh Muhammad Nuru Khalid

0 642

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sheikh Muhammad Nuru Khalid babban malamin addinin Musulunci na Sunni (IZALA) a Najeriya, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters a Babban Birnin Tarayya. Shi ne ya kafa Cibiyar Bincike ta Musulunci da Gidauniyar Da’awah wato IRDF kuma babba daga a cikin jagorarin masu zabar Limamai a  FCT a shekarar 2014.

An haifi Nuru Khalid a ranar 1 ga Oktoban 1960 a garin Jos dake  Jihar Filato. Ya taso cikin dangi masu rufin asiri, mahaifinsa malamin addinin Musulunci ne. Kafin ya tafi Makarantar Firamare Mahaifinsa ya koya masa yadda ake karatu da rubutu na Larabci. Yana dan shekara shida, ya haddace Al -Qur’ani da wasu Wakokin Larabci. Ya halarci makarantar firamare ta LA wadda yanzu ita ce makarantar firamare ta LGE a jihar Filato.

Bayan mutuwar mahaifinsa, Bai halarci Makarantar Sakandare ba. Amma mahaifiyarsa ta tallafa masa don shiga Makarantar Nazarin Addinin Musulunci ta Jamatul Izalatul Bidia Wa Ikhamatul Sunnah da aka fi sani da Izala.  Bayan kammala karatunsa ya je ya karanci karatun Islamiyya a Jami’ar Jos.

A lokacin ƙuruciyarsa, yayin da yake karatu a Jami’ar Jos ya yi aiki a matsayin malami a Makarantar Koyar da Addinin Musulunci a Jos. Ya zama Limamin Masallacin Juma’a na Kongo Junction a Jos. An nada shi limamin Jumu’ah a Masallacin Jumuat na Nyanya dake Abuja.

A shekarar 2007 aka nada shi Babban Limamin Masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters a Abuja. Saboda Masallacin yana da tasiri ya zama mai magana da yawun Jama’a, yana Khutbah a Sallar Juma’arsa a gaban mutane sama da 5,000 da kuma  Tafseer na Ramadan na shekara -shekara wanda ake watsawa a Talabijin, gidajen Rediyo da intanet kai tsaye tare da masu kallo a Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Shine wanda ya assasa Gidauniyar Da’awah Foundation IRDF.

Ya yaba wa Dokar Najeriya da Shugaban kasa saboda kin halatta auren jinsi a Kasar, wanda ya ce hakan ya sabawa koyarwar Musulunci da Kiristanci kuma ya sabawa ka’ida da kimar al’ummar Najeriya. Ya yi nuni da cewa auren jinsi guda zai lalata tsarin Haihuwa. Ya jinjinawa Gwamnatin Najeriya saboda hana auren jinsi kuma ya shawarce su da su ci gaba da aiki tare kan batutuwan cikin lumana, hadin kai da fahimta

A shekarar 2014 bam din Nyanya ya jagoranci tawagar Limaman Babban Birnin Tarayya zuwa Asibitoci kuma ya ba da kayan agaji ga wadanda abin ya shafa a madadin Musulmin Abuja kuma ya yi Allah wadai da lamarin.

“Muna gode wa Allah Madaukakin Sarki da Ya rayar da wadanda ke raye; muna karfafa musu gwiwa su dage kan imaninsu. Al’ummar Musulmin Abuja ba su ji dadin wannan lamari ba, muna addu’ar Allah ya tona asirin duk wadanda suke cikin irin wannan mugun aiki kuma adalci ya tabbata. Dukkan mu daya ne a Najeriya, kirista ne ko musulmi, sannan muna kuma jinjinawa Gwamnatin Tarayya kan duba lamarin ”

Wani dan gajeren bidiyonsa inda yake bayani akan muhimmancin almajirai inda yake cewa almajirai kamar kowa suke harda shugaban kasa.

Sheick Nuru Khalid Bayani Akan Yancin Almajirai

Sheikh Khalid ya la’anci ta’addanci da tayar da kayar baya da sunan addinin Islama. Ya bayyana cewa rashin aikin yi da cin hanci da rashawa sune manyan abubuwan da ke haifar da rashin tsaro a Najeriya sannan ya yi kira ga Gwamnati da ta kara samar da ayyukan yi ga matasa.

Sheikh Muhammad Nura Khalid mutum ne mai iyali, ya auri mata hudu yana da yara ashirin da takwas da jikoki biyar. Muna fata Allah yatsare mana Mal. Ya kuma bashi nisan kwana amin.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »