Akwai harsuna 525 da ake amfani dasu a Najeriya. Amma Harshen da ƙasa ke amfani da shi, shine Turanci, tsohon harshen mulkin mallaka ne na kasar Birtaniya. Kamar yadda aka sanar a shekarar alif ta 2003, mutane sama da miliyan 100 suna magana da harshen Turancin Najeriya a matsayin harshen na biyu.
Yin mu’amala ko kuma magana da Yaren Ingilishi yafi yawa a birane, fiye da yadda ake amfani da shi a karkara.
Babban harshen dake da yawan mutane shine Yaren Hausa wanda yake da mutane fiye da miliyan 40, mabiyansa kuwa shine, Yarabawa suna da mutane fiye da miliyan 42, sai kuma mai biye masa Yaren Igbo (Inya murai) nada jama’a kimanin miliyan 40, sai kuma Fulani (Fulfulde) da yawansu yakai miliyan 15, sai Ibibio da yawansu ya kai miliyan 10, sai kuma yaren Kanuri da yawansu yakai miliyan 8, sai Tibi miliyan 4.
Sai kuma kimanin Miliyan 2 zuwa 3 daga cikin kowanne yare a wadannan: Edo, Igala, Nupe, Izon da Berom.
Gaskiya wannan Abu yayi
[…] post Adadin Harshen Da Ake Amfani Dasu a Najeriya Da Kuma Jama’ar su. appeared first on Alummar […]