Kunun Tamba Kunu ne mai dadin gaske wanda ke dauke da sindarai masu dubin yawa ciki har da sindarin kara karfin gani da kuma sauran su. Wannan dalili yasa shafin Alummarhausa ya kawo muku wannan kunu.
YADA UWAR GIDA ZATA TANADA
- Gyada Kofi Biyu,
- Kofi Biyu Na Garin Tamba,
- Rabin Kofi Na Shinkafa,
- Lemon Tsami,
- Sukari.
YADDA UWAR GIDA ZATA HAƊA:
Da farko uwar gida zata zuba gyadar da muka ambata a baya a ruwa ta kwana yadda zatayi laushi sosai, sai a wanke dattin a nikata a blender kokuma wani abun nukawa.
Bayan angama sai a taceta sosai rariya, saiki zuba tacacen ruwan a tukunya ki fara dafawa, saiki kawo shinkafar ki ki wanke ki zuba a ciki kici gaba da saka wuta har sai shinkar tayi laushi.
Saiki kawo garin Tamba dinky ki zuba ruwan sanyi kidan dama shi sosai, saiki dinga zubawa a tukunyar da ragowar kayanki ke ciki kina juyawa a hankula har sai yayi kaurin da kike so, ki sauke a zuba a kofi a sanya dan ruwan lemon tsami da sukari, za’a iya saka madara idan ana buƙata asha dadi lafiya.