Hafsat Ahmad Idiris wacce akafi sani da Hafsa Idris, na daya daga cikin shahararun Yan wasan Hausa na Kannywood.
An haifi Hafsat Idris, ranar 14 ga watan Julin shakarar alib 1987 a garin Shagamu dake jihar Ogun a Najeriaya. Iyayen Hafsa Idris “yan asalin Jihar Kano ne dake Najeriya.
Kafin zama daya daga cikin jaruman Hausa, Jaruma Hafsat Idris “yar kasuwa ce yayin da take gudanar da kasuwancinta a Oshogbo zuwa Kano, kasancewar samun nasarar ta a kasuwancin ta sai Jaruma Hafsa Idris taji sha’awar shiga cikin harkar fim.
Hafsat Idris ta fara shirin fim din Hausa a 2016 yayinda aka fara haska ta a wani fim mai suna Barauniya da Makaryaciya da wasu fina finan dayawa tare da da Jarumi Ali Nuhu.
Hafsat Idris ta mallaki kamfanin samar da finafinan Hausa mai suna Ramlat Investment, kuma ansamar da fina finai masu yawa ciki harda wani fim mai suna Tagwaye tare da Jarumai irinsu Ali Nuhu, Sani Danja dakuma kanta.
Hafsat Idris tasamu kyaututtuka da dama cikin harkar fina finan Hausa.