Hanyoyin da Zaa bi Wajen Rage Kiba Kashi na Biyu.

0 344

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Mun sanya hanyoyi kala-kala da yan uwa zasubi su rage kiba a wannan shafi namu na AlummarHausa, wanda wasu sunyi amfani dasu sun samu sakamako mai kyau wasu kuma suna bukatar a kawo musu wata hanya don dada jarrabawa.

To masha Allah a wannan karo na uku saiku nemi wadannan abubuwa kamar haka:

Tafannuwa 4 ko 5,

Tafannuwa
Tafannuwa
  • Citta Mai Kyau,
  • Lemon Tsami,
Lemon tsami
Lemon sami
  • Zuma.

Yadda Zaku Hada:

Zaku samu tafanuwarku masu kyau manya kamar 4 ko 5 saiku dan samu wani abu kamar turmin karfe ko wani abu mai kyau da zaku iya daka wannan tafarnuwar taku, saiku dakata sosai. Saiku kawo tafashashen ruwan zafi ku zuba a kofi, ku kawo wannan Tafarnuwa ku zuba a cikin ruwan zafin.

Saiku kawo danyar citta dinku mai kyau ku bareta, kodai ku zuba bayan kuna yanyankata kanana kanana, kokuma kudan dakata kamar yadda kuka daka tafarnuwa dinku saiku zuba a cikin ruwan zafinnan.

Sai lemon tsaminku mai kyau guda daya ku yankashi ku zuba a cikin kofin ruwan zafinku. Ku zuba zuma cokali 1 ko biyu 2 saiku juya sosai, ku rufe tsawon mintuna goma. Saiku tace da rariya ku shanye. Zakuyi haka a duk safe. Insha Allahu zau samu biyan bukata.

Abin Lura:


Idan baku samu danyar citta ba zaku iya samun wacce ta bushe, saiku dakata ku tafasa ruwan da ita saikuzuba ragowar kayan hadin idan yadanyi mintuna goman saiku tace ku shanye.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »