MUFIDA ADNAN (MOOFY) MAWAƘIYA, MAI FASSARA FINA FINAN INDIYA ZUWA HAUSA
An haifi Mufida Adnan da akafi sani da Moofy a Shekarar alib 1994, a cikin Birnin Kano. Moofy ta shahara a fanin waka da kuma fassara Film din India zuwa Hausa tare da Kamfanin Fassar na Algaita.
RAYUWAR TA.
Tauraruwa Moofy tayi karatunta na Firamari a cikin Birnin kano, sannan ta kammala karatunta na Sakandire a Brain international School dake Dorayi duk a cikin Birnin Kanon Najeriya, bata tsaya a nan ba moofy ta wuce karatun Digirin a Asibitin Mallam Aminu Kano inda take karatunta a fanin Lafiya.
WAƘA DA FIM
Haka zalika Moofy tafara waƙa tun a shekarar 2011 a ƙarƙashin kamfanin ajiya na Algaita wato (Algaita records), bata tsaya a iya nan ba kasancewar daukakar Kamfanin nasu na Algaita sai tararuwa Moofy ta shiga fassarar fina finan Indiya zuwa Hausa a ƙarƙashin Kamfanin Fassara na Algaita wato (Algaita Dubstudio) a shekarar 2012.
WAƘOƘIN DA TAURARUWAR TAYI TARE DA FASSARAR FINA FINAN TA.
Moofy tayi waƙoƙi guda goma shabiyar (15) ƙarƙashin Kamfanin ajiya na Algaita wato (Algaita Record), haka zalika ta fassara Fina Finan India zuwa Hausa sama da guda Dari (100).
Cikin gwagwarmayar da tai cikin waƙoƙinta Moofy ta shaidawa AlummarHausa cewa waƙar datafi burgeta ita ce My Fantasy da kuma ƙaunarka. Haka kuma ta shaida mana cewa waƙar datafi bata wahala wajen yinta itace Masuburbudar Chasu domin tace waƙar ba irin salon waƙoƙin data saba dashi bane
LAMBOBIN YABO DA TAURARUWA MOOFY TA SAMU.
Moofy ta samu lambobin yabo dana girmamawa da dama daga ƙungiyoyi da kuma Makarantu, daga ciki sun hadar da:
- A Shekrar 2015 Moofy ta samu nasarar zama Mace ta farko a Arewa ta R&B, daga AMMA wato (Arewa Music and Movie Award).
- Sai wata kyautar girmamawa daga Daliban FCE Kano.
- Haka zalika a shekarar 2019 Moofy tasamu Lambar girmamawa daga ƙungiyar Taurarin Arewa , inda suka bata Best Female Artist. Da kuma sauran kungiyoyi da dama.
KO TAYI AURE?
Haka zalika a tattaunawar da mukai a ranar Alhamis 19 ga watan 6 2020 , Moofy ta shaidawa AlummarHausa cewa bata da Aure.
Gaskiya ina sonta tunda batada aure nikuma ina son aure