DOMIN KARIN LAFIYA:
Cokali daya na man habba a hada da zuma cokali daya asha kafin aci abinci sau biyu (2) a rana – dare da rana.
HAWAN JINI:
A hada Cokali daya na garin habba dana zuma gangariya, Sa’annan asanya tafarnuwa dakakka amma ‘yar kadan. Asha kafin aci abinci na tsawon kwana ashirin (20).
CIWON DASASHI DA HAKORI:
A tafasa garin habba da ruwan khal (vinegar), Awanke baki dashi.
TSUTSAR CIKI:
Asha habba tare da ruwan khal daidai gwargwado, Tana kashe tsutsar ciki sosai.
RASHIN BACCI:
Asanya habba cokali daya a cikin kofin shayi asha kafin a kwanta bacci misalin (awa daya kafin a kwanta).
RASHIN GANI DA KYAU:
A zuba cokali daya na man habba a cikin carrot juice asha Kullum har tsawon wata daya.
TARI DA ASMA:
Ashafa man habba (ko kuma Habba rob ) a kirji da dare kafin a kwanta bacci.