An haifi Sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero ne a shekarar alib 1961. Kuma Da na biyu ga marigayi Ado Bayero. Ya halarci makarantar firamare ta Kofar Kudu a karamar Hukumar binni wato (Kano Municipal), daga nan kuma ya tafi makarantar sakandare ta birnin Kudu dake jihar Jigawa a yanzu.
Bayan Kammala Makarantar Sakandire dinsa ne Kuma, Alh Aminu Ado Bayero ya tafi Jami’ar Bayero dake Kano inda ya samu digiri a fannin sadarwa.
Har ila yau, Alh. Amin Ado Bayero ya yi karatu a makarantar Aviation Oakland da ke California, Amurka, ya kuma yi aikinsa na bautar kasa wato National Youth Service Corps (NYSC) a Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA) dake Makurdi, a Jihar Benue.
Bayan hidimar sa ta bautar kasa, Alh. Amin Ado Bayero yasamu aiki a kamfanin Kabo Air Limited.
Alh. Aminu Ado Bayero an nadashi mai rikon mukamin ne a matsayin Dan Majen Kano hakimin Dala a shekarar alib 1990 lokacin da mahaifinsa wato marigayi, Ado Bayero ya yi bikin cikarsa shekaru 60. A wannan shekarar, Kuma mahaifinsa marigayi ya aura masa mata biyu a lokaci guda.
Sabon Sarkin ya rike mukamai na gargajiya da yawa kafin a naɗa shi Sarkin farko a Masarautar Bichi. Ya fara ne a matsayin Dan Majen Kano, sannan Danburan Kano, Turakin Kano, Sarkin Dawaki Tsakar Gida sannan Wamban Kano.
A ranar 9 ga watan Maris 2020, an nada shi a matsayin sarki Kano, Sarki na 15 na Masarautar jihar Kano, don maye gurbin Muhammad Sanusi II, wanda aka hambarar da mulkinsa a wannan ranar.