Sarkin Kano Muhammadu Bello Dan Dabo (1882 – 1893) 1

1 1,908

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Malam Muhammadu Bello dan Sarkin Kano Malam Ibrahim Dabo ne, shi ma Malama Shekara ta haife shi,” kanin Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi da Sarkin Kano Usman Maje Ringim ne.

Bayan Sarkin Kano Abdullahi Maje Karofi ya rasu acikin shekara ta 1882, sai aka zabi Muhammadu Bello ya gaje shi.

A lokacin wannan zabe duk hanyoyi na al’adun zaben sarki an yi amfani da su, kuma daga baya ya sami amincewar Sarkin Musulmi.

A lokacin da aka nada Muhamimadu Bello ya riga ya tsufa, sannan ga shi da tarin gogewa a kan makamar mulki da iya hulda da jama’a.

Sarkin Kano Muhammadu Bello ya yi nade-naden sarauta, ta haka ne ya nada babban dansa Muhammadu Tukur ya zama Galadiman Kano.

A zamanin mulkin Sarkin Kano Muhammadu Bello rigingimun na cikin gida da na waje sun dabaibaye shi haikan. Sarki Muhammadu Bello sai da ta kai yana karbar zuga da tawaye Wadannan matsaloli na cikin gida da na waje ba su bar Sarki Muhammadu Bello yayi wani tasiri na zahiri dangane da iya gudanar da wasu ayyuka a masarautarsa ba. duba da yakin da aka yi da kasar Kila a zamanin Sarkin Kila Amadu.

A zamanin Sarkin Kano Bello an ce Kila ta bi Dutse, wata rana sai Sarkin Dutse Bello ya kira Madakin Kila Amadu ya ce ya je su sadu a Dutse. A yayin nan kuwa Kila ta fara bunkasa, sai Madakin ya ce, bai kamata ya je ba, sai ya ki zuwa, ya ce a sanar da Bello ba zai je ba.

Sarkin Dutse ya damu ya kai kara gaban Galadima Tukur, Galadima ya sanar da Sarki wannan kara. Sai Sarkin Kano Bello ya shirya ya hau ya tafi Kila da kansa ya sauku ya hada su tare ya yi musu sulhu kuma aka yi yarjejeniya cewa Madaki zai rika zuwa Dutse.

Da Sarkin Kano zai dawo gida suka hadu suka raka Sarki gaba daya har kan iyakar kasarsu. Kamar magana ta kare, daga nan suka dawo gida cikin Kila gaba daya, ai Madaki ya aikawa Sarkin Dutse ya ce masa, kada ma ya kwance sirdinsa ya ce zai kwana a garinsa, in kuma ya kuskura ya kwanta to, kare zai kwashi hanjinsa, Da jin haka, sai Sarkin Dutse ya biyo Sarkin Kano, ya same shi a Birnin Kudu ya sake sanar da Sarki cewa bayan sulhun da ya yi musu, Madaki bai yarda ba, ya ma hana shi kwana a garinsa.

Nan da nan Sarki ya sake aika ‘wa Madaki ya ji abin da ya faru, amma lallai gobe ya bi umurnin sarki ya tafi wurin Sarkin Dutse. Da dai Madaki ya ji Sarki ya tsananta, sai ya yi damarar yaki ya hau ya tafi Dutse. Har sun isa kofar gari za su Shiga, sai wani marokin Madaki ya fara kida yana waka yana cewa:

Baba ba Dutse Gadawur ba,
Ko da dutsen nan na nika ne


Baba a bar nikan a kan dutse.
Amadu ya sha a turmi,


Amadu koma gida
Kar ka amsa kiran kowa.


Lalle a bar nikan
Amadu ya sha a turmi.

Aksance damu a Tarihin wannan shahararen sarki na biyu.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. […] Sarkin Kano Muhammadu Bello Dan Dabo (1882 – 1893) 1 […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »