Sani Musa Danja ko kuma Sani Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Sani Danja fitaccen dan wasan Najeriya ne, mawaki kuma daraktan a fagen shirya Fina Finan Hausa.
An haife Sani Danja a ranar 20 ga watan Afrilu, shekara ta 1973 a karamar hukumar Fagge, dake Kanon, Nigeriya a gidan mahaifinsa Alhaji Musa Abdullahi da Hajiya Risikat. Shi ne babba a cikin ’ya’yan bakwai da iyayensa suka haifa.
Sunan ‘Danja’ ya samo Asali ne tun yana Kuruciyarsa saboda an ce yana da matukar taurin kai da dagewa a yarintar sa.
Sani ya halarci makarantar firamare ta Yan Sanda daga shekarar 1979 zuwa 1980, san nan ya ci gaba da makarantar sakandare ta Government Junior Secondary School Kawaji, a shekara ta 1985 zuwa 1989, ya tafi Kwalejin Rumfa don kamala karatunsa na sakandare a shekarar 1989 zuwa 1991.
Sannan yacigaba da karatunsa na gaba da secondire zuwa FCE Kano inda ya samu nasarar samun takardar shaidar NCE.
A cigaba da neman iliminsa Sani yasamu damar cigaba da karatunsa inda ya kamala karatunsa na Advance Diploma a Public Adminstration inda ya kasance a ciki har 2004.
Ya fara shiga masana’antar shirya finafinan Hausa wato Kannywood a shekarar alib 1999 tare da fim din sa na ‘Dalibai’ , fim din da ya kirkira kuma ya nuna tare da abokin aikinsa Yakubu Muhammad.
Alhaji Rabi’u K / Wambai ya kira ni ya ce kana da kyau ka shiga masana’antar fim ɗin Hausa. Bayan nasarar da yasamu ta fim dinsa (Dalibai), sai kuma wani fim mai suna ‘Adon kishiya’ a shekara ta 2000, sannan sai wani fim kuna mai suna ‘Kwarya tabi Kwarya’, babban fim ɗin da yayi tare da jaruma Jamila Haruna a shekara ta 2000.
A watan Afrilun, 2009, Sani Danja ya shiga cikin hatsarin mota a kan hanyar Kano-Kaduna, inda ya ci karo da karaya a kafarsa.