GURASAR TANDERU
KAYAN DA ZA KI TANADA
- Fulawa
- Yis
- Kantu/ridi idan da bukata
- Sikari
- Gishiri
YADDA ZA KI YI
Ki sami fulawarki ki tankade ki zuba mata yis, ki zuba ruwa ki kwaba, ka da ki kwaba shi da ruwa, ki kwaba shi da dan tauri. Idan kina son Gurasa mai sikari, sai ki zuba sikari a cikin kwabin , idan kuma kina son mai gishiri ne, sai ki zuba gishiri a cikin kwabin.
Idan lokacin zafi ne za ta yi saurin tashi saboda dama yis zafi yake so ,awa uku zuwa hudu ya ishe shi ya tashi , amma idan lokacin sanyi ne yakan dade bai tashi ba.
Idan kina so ki yi Gurasa da safe, to sai kin kwaba fulawarki tun da daddare, kuma kin nemi wuri mai dumi kin saka kin rufe sosai domin ya tashi.
Idan kin tabbatar kwabinki ya tashi , sai ki zuba karare a cikin Tanderu, ki kunna wuta domin tanderun ya yi zafi, idan kin tabbatar tanderun ya yi zafi sosai kuma karan ya cinye sai ki yayyafa ruwan kanwa a ciki, ki saka tsintsiya ki share toka-tokar data makale a cikin tanderun. Sai ki kawo kwabinki ki cura shi ya yi fadi, ki fakada da hannu , yadda dai ki ke son fadinta ya kasance, idan kina son kantu/ridi sai ki zuba dan kadan a kan gurasar a tsakiya, idan kuma ba kya so shi kenan sai kawai ki saka curin da ki ka yi a cikin tanderun , idan kin gama sakawa sai ki kawo tire ki rufe tanderun.
Ta kan dau kamar minti ashirin zuwa minti ashirn da biyar kafin tayi. Kai ba ma sai kin kalli agogo ba , da ta yi za ki ji kamshi ya turare ko ina a gidan .
Sai ki kawo wuka da tire, ki ringa saka wuka kina bambarota tana fadawa kan tiren.
Amma sai kin yi a hankali saboda zafi ka da ki kone domin tanderu yana da zafi sosai