TARIHIN MASARAUTAR KATSINA GIDAN KORAU A TAKAICE NA 2

1 1,261

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

YADDA MULKIN DALLAZAWA YA FARA A KATSINA


Daga lokacin da Ummaru Dallaje ya shiga Gidan Korau da ke Cikin Gidan, daga nan ne mulkin Dallazawa ya fara, a shekarar 1807 wanda ya kai ƙarshe a shekarar 1906.

Ummarun Dallaje, ya jaddada addinin Musulinci a ƙasar Katsina baki ɗaya, ya kafa mulki irin na tarayya, a inda aka ba malam Muhammadu Na’Alhaji kudu maso yamman Katsina a matsayin ‘Yanɗakan Katsina, mai fadarsa a Zakka da gidansa na mulki a ‘Yantaba da ke cikin birnin Katsina.

Shi kuma malam Ummarun Dumyawa, aka ba shi mulkin arewa maso yammacin Katsina, a matsayin Sarkin Sulluɓawan Katsina, mai fadarsa a Bugaje da kuma gidan Sarautarsa da ke Sulluɓawa ta Ƙofar Guga.

Shi kuma Ummarun Dallaje ya zama Sarkin Katsina gaba ɗayanta, mai babbar fadarsa a Gidan Korau da ke Cikin Gida.

Abubakar Saddiƙu shi ne ya gaji Ummarun Dallaje a shekarar 1835, wanda shi ma, ya zauna, ya yi rayuwarsa a Gidan Korau na Cikin Gida.

A zamanin mulkin Saddiƙ, an sami tawaye na Maraɗawa, wato Sarakunan Haɓe na Katsina waɗanda aka ci da yaƙi, suka koma Maraɗi. Su waɗannan Maraɗawa, sun ƙuduri aniyar dawowa Katsina, da nufin karɓar mulki daga hannun Fulani Dallazawa.

Wannan shi ya kawo yaƙe-yaƙe a tsakanin mayaƙan Maraɗawa da mayaƙan Katsina a ƙarƙashin jagorancin Abubakar Saddiƙu tare da taimakon mayaƙan kuma manyan Sarakunan fada, irin su Durɓi Giɗaɗo da Abdu Nadabo, Tarno Gajeren Badde.

Bayan rasuwar Abubakar Saddiƙu, sai Muhammadu Bello ya ɗare karaga a shekarar 1844. Shi ma, a nan Gidan Korau da ke Ciki Gida ya zauna ya yi mulkinsa.

A zamanin Bello ɗin ne, aka ƙarfafa harkokin shari’a a Katsina, aka inganta karɓar baƙi malamai da ‘yan kasuwa. Muhammadu Bello ya kakkafa sababbin jini a mulkinsa, irin Giɗaɗo, Tarno Gajeren Badde da Abdu Nadabo.

Waɗannan mutane, su ne manyan jarumai na Katsina, waɗanda suka dinga fafatawa da Maraɗawa, kuma su ne manyan fadawa masu murɗa zare a fadar Cikin Gida.

Ahmadu Rufa’i (1869-1870) da Ibrahim Muhammadu Bello (1870-1882) su ma, sun yi mulkin Katsina, kuma a nan Gidan Korau na Cikin Gida suka zauna suka rasu a nan.

A zamanin Rufa’i ne, yaƙi da Maraɗawa ya tsananta, har ma ya hana abubuwa na cigaba. Ibrahim Bello ya zama Sarki bayan rasuwar Ahmadu Rufa’i a (1870). Shi ma Ibrahim, ya gaji wannan fitina ta yaƙi da Maraɗawa, a ƙarƙashin su Ɗanmari da Ɗanbaskare.

A zamanin Sarki Ibrahim ne aka gina ƙofar shiga Cikin Gida, wato Ƙofar Soro, inda aka yi mata gini Inda ake wuchewa ta chikin kofar idan za’a Shiga gidan korau.

Bayan rasuwar Ibrahim Bello, sai Musa ya gaji Sarauta a shekarar 1882, wanda shi ma ya yi rayuwarsa a Gidan Korau na Cikin Gida.

A zamanin Musa ne mayan dakarun nan na Katsina, kuma manyan fadar Cikin Gida, irin su Durɓi Giɗaɗo da Abdu Nadabo suka rasu.

Abubakar Ibrahim ya gaji Sarauta a shekara ta 1887, wanda shi ma ya zauna a Cikin Gidan Korau na Cikin Gida.

Amma Abubakar ba a Gidan Korau ya rasu ba, domin Turawa sun tuɓe shi daga Sarauta, suka tafi da shi Ilorin, a shekarar 1925 aka dawo dashi kano a zamanin sarkin kano Usman Dan Abdullahi maje karofi ,Sarkin katsina abubakar ya rasu a kano a shekarar 1940 zamanin Sarkin Kano Abdullahi bayero.

Kamar yadda bayani ya gabata, a zamanin Abubakar ne Turawa Ingilishi suka kama Katsina, koda yake ba a yi yaƙi da su ba.


Bayan tuɓe Abubakar da Turawa suka yi a dalilin rashin fahimtar da ta shiga tsakanin Sarki Abubakar da Turawa, sai Turawan suka tuɓe shi, suka yi masa murabus, suka tafi da shi Ilorin.

Sai suka naɗa Muhammadu Yero Sarkin Katsina, wanda shi ma, ya ɗan zauna a Gidan Korau na Cikin Gida, kafin abin da ya sami Abubakar, shi ma ya same shi. Turawa sun tuhume shi da rashin iya aiki wanda a wannan dalili suka tuɓecshi, suka kai shi Lakwaja.

Wannan al’amari ya auku ne a shekara ta 1906. Wannan ne kuma ya kawo ƙarshen mulkin ƙasar Katsina da Dallazawa suka yi daga Gidan Korau na Cikin Gida.

Muhammadu Dikko, ɗan Durɓi Giɗaɗo, ya zama Sarkin Katsina na farko a tsatson Fulani Sulluɓawa. Shi Dikko, Turawa ne suka naɗa shi, ya zama Sarkin Katsina a shekarar 1906, bayan tuɓe Muhammadu Yero da aka yi.

A zamanin Muhammadu Dikko ne aka matso da ƙofar shiga Cikin Gida, wato Ƙofar Soro Inda take a yanzu, aka yi mata ginin dutse da tagogi, aka kuma yi mata bene wanda a Katsina ake kira Soro. Daga nan ne ma, ƙofar ta sami sunan Ƙofar Soro, wato ƙofa mai bene ko soro.

Daga baya, an kuma riƙa kiran ƙofar da sunan Kan-Giwa, saboda wannan soron yana kama da kan giwa da aka sani. Ƙofar an sanya mata agogo, wadda a da, take bugawa duk bayan awa guda, wadda ake jin ƙarar bugawar a ko’ina cikin birnin Katsina.

A zaminin Dikko ne, aka gyara filin da ke gaban Kan-Giwa ko Ƙofar Soro, ya zama filin yin jahi ran salla ƙara a ko babba, da kuma yi wa hakimai da jama’ar Katsina da suka taru a wurin jawabi.

A yamma da filin aka yi ofishin ‘yan doka, wanda ya zama ofishin ‘yan sanda a yanzu. A arewa da filin Kan-Giwa ko Ƙofar Soro, aka gina ɗakunan shari’a na Alƙali Babba da Alƙali Ƙarami, wanda kafin wannan lokacin, a zauruka ake yin shari’ar.

An kuma gina sakatariya ta ma’aikatan En’e ta Katsina. A kudu kuwa, da filin na Ƙofar Soro, aka gina ma’aikatar wakshof inda ake yin ƙere-ƙere. A can gaba da ma’aikatar aka gina babban masallacin Juma’a na uku a Katsina. Dikko ya yi gaba ɗayan rayuwarsa a Gidan Korau da ke Cikin Gida, kuma ya rasu a nan a shekarar 1944.

Wanda ya gaji Muhammadu Dikko shi ne ma kamar mahaifinsa, ya zauna a Gidan Korau. A zamanin Usman Nagogo, an ƙarfafa bayar da ilmin boko da buɗe makarantun boko a birni da ƙauye na faɗin ƙasar Katsina.

Sarki Usman Nagogo ya rasu a shekara ta 1981. Wanda ya gaji Sarki Usman, shi ne Muhammadu Kabir Usman a shekara ta 1981.

A zamanin mulkin Kabir Usman ne, ƙasar Katsina ta sami Jihar kanta a shekara ta 1987, wanda a dalilin haka, garin Katsina da wurare da dama a Jihar, suka sami ci gaba.

Abdulmumin Kabir Usman, shi ya gaji mahaifinsa a matsayin Sarki. Kamar sauran Sarakunan Katsina, shi ma a Gidan Korau na Cikin Gida yake zaune.

ABIN LURA NA DAYA: a nan, game da Gidan Korau na Cikin Gida shi ne, duk ilahirin Sarakunan Katsina, tun daga Haɓe na zuriyar Korau na Wangarawa, har zuwa Fulani Dallazawa, zuwa Fulani Sulluɓawa, dukkaninsu a Gidan Korau ɗin ne suka zauna, suka yi Sarauta, kuma wata ƙila, suka rasu a nan, in ka ɗebe Abubakar Saddiƙu wanda aka tuɓe daga Sarautar Katsina, aka tafi da shi ƙasar Sakkwato, da Abubakar Ibahim da Muhammadu Yero waɗanda Turawa suka tafi sa su wani wuri na daban.

ABIN LURA NA BIYU: shi ne, Gidan Korau wanda aka gina a farko-farkon ƙarni na goma sha biyar, yana da wajen shekara dari biyar (500) da ginawa.


Daga:

M.T.SAFANA ARCHIVES

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Naziru Sanusi Nazee Rty says

    Gaskiya Allah ya saka muku da Alkhairi, a matsayina na dan Jihar Katsina yau na samu cikakken Tarihin Masauratar Katsina. Duk da dai ni ina Masarautar Daura ne

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »