Hausapeoples
Tarihin garin Kura ta jihar kanon Nigeria 🇳🇬 mai sauraro asha karatu lafiya.
GARIN KURA
Garin kura ya samo asali ne a kan shahararren Kogin da ake kira Rafin Kura a kudancin garin, wanda ake yin amfani dashi don aikin noma da kuma shayar da dabbobi, ƙarni da suka wuce. Babu shakka yana da matukar wuya a samu ainihin shekara ko zamanin da mutanen Kura suka zauna a wannan ƙasa mai ban sha’awa.
Amma abin da aka sani shi ne cewa, Kura ta zo ne a cikin karni 18 bayan an gano ta a matsayin hanya da kuma sansani na Larabawa da Abzinawa da yan kasuwa.
A wannan lokacin, ana samun mutane ne kawai a wuraren kamar Alkalawa, Limamai, Yalwa, Rimin Daddo, Unguwar Gandu, Unguwrar Bugu da dai sauransu.
A wannan lokacin kasuwancinsu na gida shine ya hadar da aikin Gona, Kasuwanci, Saƙa, Rini, da kuma farauta. Sannan suna samar da Rawani (Rawani Dan Kura) a gida.
Rawani dai Sarakunan gargajiya sun yin amfani da Rawani, dattawan maza, masu arziki da kuma malaman Islama.
An san mutanen Kura ta hanyar ƙarfin zuciya da kuma sadaukar da kai ga wadannan al’adu nasu na gida. Fiye da kashi 99% na duka yawan jama’ar dake Kura Musulmai ne kuma mafiya yawa Hausawa ne, sai Fulani, da kuma Kanuri.
Garin ko wurin nada sararin ƙasa mai ban sha’awa da kuma kyau wajen yin shuke-shuke masu kyau.
Saboda haka, Kura na daya daga cikin kananan hukumomi 44 a yankunan Jihar Kano da ke a kudancin jiha, garin nakusa da Babban titin Hanyar Zaria-Kano wadda yake da nisan kimanin muraba’i 35Km daga babban birnin jihar. Ya kasance a 11 46 ’17 “N zuwa 8 25’49 “E.
Sannan jihar nada girman kasa da yakai kimanin muraba’i 206km (80 sq mi) na ƙasa mai cinye tare da yawan Jma’ar da yakai kimanin 144,601 a kidayar shekara ta 2006. Har ila yau, yana hannun Riga KO iyaka tare da Garun Malam a yamma kuma , yankin Madobi daga Arewa, Yankin Dawakin Kudu daga Gabas Bunkure kudu.
Haka zalika yanzu haka mutanan Kura kashi 80% cikin Dari manoma ne inda suke samar da kayan gona Rani da Damuna
Wasu daga cikin albarkatu Gona daKur ke samarwa a yankin su ne Shinkafa, Alkama, Masara, Gero, Masara, Tumatir, Albasa, Kokwamba, Kabeji, da dai sauransu.
Karamar Hukumar Kura nada unguwani kamar haka:
1. DALILI,
2. DAN HASSAN,
3. DUKAWA,
4. GUNDUTSE,
5. RIGAR DUKA,
6. KARFI
7. KOSAWA,
8. KURINSUMAU,
9. SARKIN KURA,
10. TANAWA