Yau kusan shekaru 19 kenan da duniya ta rasa mutumin daya kirkiro ya kuma kawo sauyi a hidimar kidan kalangu a kasar hausa.Bama ana zato ba, a’a a fagen wakar hausa ba wani a gabansa har ya zuwa tatassara. Shata, Duna na Bilkin Sambo. Koda yake akwai mawaka da sukayi zarra a zamaninsa amma hada basirarsa da tasu tamkar hada hasken kyandir ne da hasken rana.
A tsakanin 1936 da 1999,watau farawa da gama wakarsa(ko kuma tsakanin wakarsa ta farko:
‘Yammaza Allahn fara bama.’ da Wakarsa ta karshe:
’Dankabo Jarmai Mamman.’,
wadda yayi lokacin nadin Alh. Ummaru Musa Gwabnan Katsina ranar 29/5/1999).
Shata yayi wakoki kimanin abinda ya dara 8,000. Dalili shine an taba rutsa shi a gida Funtuwa aka tambayeshi ko nawa ne wakokin Alhaji? Sai yace baya iya ganewa amma yasan tun sa’adda ya fara yayi wakoki kundi-kundi har kundi sama da 40, kuma a cikin kowanne kundi yana da waka sama da 200. In ka tara kaga zaya baka jimillar da aka bayyana a sama.
Zanso in dan tazgada kadan in nazarci abinda mawaka suka kira ‘sare’ a waka, wanda da shi mawaka sukayi ta aron wakokinsa suna gina nasu kalmomin..’Sare’ a waka na nufin ka ari waka ko wani sashe na wakar wani mutum ka maishe shi naka.
Amma saboda wasu mawakan ma suna da basira wadda take da amfani kwarai sai kaga wasu lokuta kalmomoin Shatan da nasu sunyi kamanni da juna.
Akwai da dama a inda wakokin makadin da na wasu sukazo iri daya. Misali, a cikin 1940 Bawa makaho mai ganga na Gorar Fata ya saukar wa Indon Zara, wata budurwa da tayi tashe, diyar maigarin ‘Yammama. Anan ya sami labarin wani bakon mawaki waishi Shata ya bulla Ketare. Bayan wasan ‘Yammama ya kare suka fusata suka doshi Ketare don su kai ma Shata caffa su yakeshi.
Suna sauka Ketare sai bama bata lokaci gaba daya suka zama yaran Shatan. Kwana biyu a Ketare ana wasa. Da zasu koma gida sai Shatan ya yi tsalle ya bisu. Ya tafi dasu saboda a dan zaman da sukayi da shi a Ketare ya shaku da Bawa sosai.
Wata rana a Gora sai ga wani direba daga Jikamshi yazo daukar Bawa don yin bukinsa, na auren wata yarinya, Hauwa ‘yar Tsohuwa. Aka dauke su aka tafi dasu.
Zaka iya Karanta :