A Labari marar tabasa da ya gabata a baya, Bayajidda Yarima ne a Kasar Baghdad ( Bagadaza) (Birnin Iraq) kuma shi Da ne ga sarki Abdullahi, An tilassa Bayajidda yabar Kasar bayan cinye Kasar da yaqi da wata sarauniya Mai suna Zidam Wada ake kira da suna Zigawa tayi da yaqi, bayan yabar Kasar (Bagadaza) sai yay yankin Africa tare da Dubin mayaka masu tarin yawa ya sauka a Barno.
Lokacin da Bayajidda ya sauka ƙasar Barno, ya iso ƙasar da runduna mai ƙarfi wacce shi sarkin Barno ya kalleta a matsayin barazana ga mulkinsa. saboda haka sai ya shiga shawara da wazirin sa bayan gama shawarar ne suka yanke cewa Sarki zai aurwa Bayyajidda Yarsa ta yadda zasu samu damar mallake tawagar mayakan da bayajidda yake dasu, Saboda wannan dalili sai shi sarkin Barno na wannan lokacin ya fara tunanin yadda zai yi ta cikin dabara ya zama ya mallake jama’ar Bayajidda sannan shi kuma ya sallame shi daga garin (ya koreshi) . Wannan tunani na sarkin Barno ya haifar da aurar da ‘yarsa mai suna Magaram wace ake kira da Magira ga Bayajidda.
Faruwar wannan aure tsakanin Bayajidda da wannan ‘ya ta sarkin Barno ta haifar da kyakkyawar dangantaka tsakanin Bayajidda da wannan sarki na Barno, wanda har ta kai ga Bayajidda yakan haɗa rundunarsa da ta sarkin Barno su je yaƙi domin kare daular Barno a duk lokacin da buƙatar hakan ta faru.
wannan dangataka kuma ta baiwa shi sarkin Barno damar mallake jama’ar Bayajidda, wanda haka kuma ta haifar da Bayajidda yana fuskantar barazana ga rayuwarsa, wanda hakan ta saka dole ya bar daular ta Barno Cikin dare.
Bayajidda ya baro garin Barno shi da matarsa ya nufo yamma, bai zame ko’ina ba sai wani gari da ake cewa Garun Gabas, wanda yanzu garin yana ƙarƙashin mulkin masarautar Haɗeja.
A wannan gari wasu maruwaitan suka ce ya bar matar tasa da ciki ta haifi ɗa namiji, A wannan gari ma dai Bayajidda hankalinsa bai kwanta ba, saboda yana ganin kamar za a iya biyo shi daga garin na Barno, saboda haka sai ya ƙara tafiya yamma inda ya sake yada zango a garin Gaya.
Bayan ya zauna a wannan gari na Gaya, ya hadu da makera suka kera masa wuka sai kuma ya ci gaba da tafiyarsa ya sauka a garin Daura ta (Jihar Katsina) da shigarsa ya sauka a gidan wata tsohuwa, sai ya bukaci tabashi ruwa don yasha sai tace babu ruwa kuma rijiyar da suke debowa akwai wata macijiya Mai suna “Sarki” Wanda bata bari a debi ruwan Cikin wannan rijiya sai a Sati sau daya suke diba, Dajin wannan batu na wannan tsohuwa nan take ya umarci a nuna masa wannan rijiya tsohuwa ta nuna masa rijiya. Da zuwan Bayajidda ya kashe wannan macijiya ya kuma sare kanta da wukar da makera sukai masa.
Bayan yasha ruwan ya isheshi sai kuma ya dauki kan Macijiyar yasanyashi acikin jakarsa ya koma gidan tsohuwar (Wanda yanzu haka Rijiyar tazama abin kallo).
Karanta: